Satar kudi: Tsohon Shugaban EFCC Magu, ‘CP Singham’, da Minista za su yi wa Maina shaida

Satar kudi: Tsohon Shugaban EFCC Magu, ‘CP Singham’, da Minista za su yi wa Maina shaida

- Babban kotun tarayya ta gayyaci mutum 10 su bada shaida a kan Abdulrasheed Maina

- Alkalin kotu ya aikawa Ibrahim Magu, Abubakar Malami, Femi Falana goron gayyata

- Ana shari’a da Abdulrasheed Maina, ana tuhumarsa da wawurar kudi Naira Biliyan 2.1

Babban kotun tarayya da ke Abuja ta gayyaci mutane 10 su bada shaida a shari’ar zargin badakalar da ake yi wa tsohon shugaban PRTT, Abdulrasheed Maina.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN su na cikin masu bada shaida a kotu.

Haka zalika babban lauya mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana zai bada shaida a gaban Alkali.

Ana zargin Abdulrasheed Maina da kamfaninsa na Common Input Property and Investment Ltd da laifin karkatar da kudin da su ka haura Naira biliyan biyu.

KU KARANTA: Shugaban EFCC ya je kotu, ya bada shaida a shari'a

An gayyaci wadannan mutane su bada shaida a shari’ar tsohon shugaban kwamitin gyarar harkar fansho ne bayan rokon da wani lauyan Maina ya gabatar.

Sauran wadanda aka aika wa goron gayyatar bada shaida sun hada da M. Mustapha, darektan bin ka’idoji da sharudan aiki na babban bankin Najeriya watau CBN.

Akwai Ibrahim Kaigama na ma’aikatar NIPSS, Cif Kenneth Amabem da ke birnin tarayya Abuja, da kuma G.T. Idris da Hassan Salihu da su ke aiki a hukumar ICPC.

Har ila yau cikin wadanda za su bada shaida akwai tsohon kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Wakil.

KU KARANTA: Abin yi idan an turo maka makudan kudin da ba ka san da su ba

Satar kudi: Tsohon Shugaban EFCC Magu, ‘CP Singham’, da Minista za su yi wa Maina shaida
Malam Abdulrasheed Maina Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wannan gayyata ta fito ne daga ofishin Alkali mai shari’a Okon Abang a ranar 8 ga watan Maris, 2021. Za a saurari zuwan wadannan mutane zuwa kotun tarayyar.

Ministan shari'a na tarayya, Abubakar Malami ya fito ya yi karin haske game da rade-radin da yake yawo, ya ce ba ya binciken tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu.

Ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya ce babu binciken da ya ke yi a kan Bola Tinubu.

Abubakar Malami ya ce amma bai sani ba ko hukumomin EFCC da CCB su na binciken fitaccen ‘Dan siyasar, kuma daya daga cikin manyan kusoshin jam'iyyar APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng