2023: Gwamna Bello ya daina kame-kame, ya fadi abin da ya sa zai shiga takarar Shugaban kasa

2023: Gwamna Bello ya daina kame-kame, ya fadi abin da ya sa zai shiga takarar Shugaban kasa

- Gwamnan jihar Kogi ya tabbatar da cewa zai nemi kujerar shugaban kasa

- Yahaya Bello ya ce 2023 ta matashi ce ba wai ‘Dan Arewa ko ‘Dan Kudu ba

- Gwamnan yake cewa marasa galihu daga cikin al’umma ne su ka turo shi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya fito ya tabbatar da cewa babu shakka ya na da niyyar neman kujerar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.

A yau jaridar PM News ta rahoto gwamnan ya na wannan bayani lokaci mai tsawo bayan wa’adin da wasu kungiyoyin matasan kasar nan su ka ba shi ya shude.

Da yake magana da ‘yan jarida a garin Abuja, Alhaji Yahaya Bello ya ce ba zai yi garaje ba, zai jira har lokacin da za a buga gangar siyasa kafin ya shiga takarar.

Ya ce: “Ba na daukar wannan a matsayin takarata. Takara ce ta matasa, masu taso wa, mata, marasa galihu, marasa karfi da wadanda ake danne wa a al’umma.”

KU KARANTA: Kusoshin APC sun ba Bello/Umahi shawarar neman shugaban kasa

“Wadannan su ne mutanen da ke kiran in zo in bauta wa kasa, in fito neman takarar shugaban kasa a zaben 2023. Saboda gudun saba doka, zan jira sai lokaci ya yi.”

“Kuma magana ta gaskiya ita ce a cikinsu na fito, gidan masu karamin karfi, kuma ga ni matashi.”

Yahaya Bello ya ce marasa hali da masu karamin karfi da wadanda ake zalunta sun taso shi gaba a kan ya yi takarar, don haka yake ganin ba zai iya ba su kunya ba.

Gwamnan ya sake yin fatali da kiran da ake yi na cewa ya kamata mulki ya koma Kudu, ya ce babu wata yarjejeniya ta kama-kama a tsarin mulkin jam’iyyar APC.

2023: Gwamna Bello ya daina kame-kame, ya fadi abin da ya sa zai shiga takarar Shugaban kasa
Gwamna Bello da Shugaban kasa a Lokoja Hoto: www.newsexpressngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Abin da ya sa har yanzu ba a gaFani-Kayode a APC ba - Bello

“Na yi imani cewa matasa su na da lakanin da za su iya gyara kasar nan, maganar matasa ake yi, ba batun Kudu, Arewa ko wane Musulmi ne ko Kirista ba.” Inji Bello.

Wasu su na ta ba gwamnan shawarar ya nemi kujerar shugaban kasa a 2023, kuma tun tuni fastocin takarar Yahaya Bello su ka fara yawo a wasu jihohin Najeriya.

Kwanaki har an ji yadda wata kungiyar magoya bayan Yahaya Bello mai suna PYB FRONTIERS ta yi kira ga mutanen Najeriya da su marawa gwamnan baya a 2023.

Wannan kungiya ta bukaci mutane su tabbatar cewa Bello ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel