Yahaya Bello: Abinda ya sa har yanzu ba a ga ‘danuwana’ Femi Fani-Kayode a APC ba

Yahaya Bello: Abinda ya sa har yanzu ba a ga ‘danuwana’ Femi Fani-Kayode a APC ba

- Kwanaki Yahaya Bello ya fito ya na cewa Femi Fani-Kayode zai dawo APC

- Har yanzu babban ‘dan adawan bai bar PDP ba, ya fito ya karyata maganar

- Yahaya Bello ya yi karin haske a game da alakarsa da fitaccen ‘dan adawar

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya yi bayanin abin da ya sa tsohon Ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, bai koma APC ba.

Alhaji Yahaya Bello ya yi karin haske ne a lokacin da aka gayyace shi a cikin shirin siyasa na Politics Today da ake yi a gidan talabijin na Channels.

Gwamna Bello ya bayyana cewa shi da tsohon Ministan na PDP tamkar ‘yanuwan juna ne, ya kuma bada labarin yadda zamansu ta canza masa ra’ayi.

A cewar Yahaya Bello, ko da Fani-Kayode bai tsere daga jam’iyyar PDP ya koma APC ba, wannan ba zai hana su kokarin da su ke yi na dinke-baraka ba.

KU KARANTA: Femi Fani-Kayode ya sauya sheka jam'iyyar APC - Yahaya Bello

Gwamnan ya ce: “Ni da Cif Fani-Kayode, ‘yanuwan juna ne, kuma mu na kokarin tabbatar da an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar nan.”

Bello yake cewa “Femi Fani-Kayode da kowa ya sani, ya samu canjin zuciya bayan haduwarsa da ni. Ina tunanin ya sake tunani a game da matsayar Najeriya."

Yahaya Bello ya cigaba: “Ku na gani, mun samu mun iya yin sulhu da kungiyar gamayyar ‘yan kasuwan Arewa da kuma sauran fusatattun ‘yan uwanmu.”

“Kin shigarsa APC zabinsa ne, haka kin shigowarsa, sabanin ra’ayin siyasa bai da tasiri wajen kokarin neman zaman lafiya da hadin-kai da mu ke yi.” Inji sa.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya rabu da Mai dakinsa

Yahaya Bello: Abin ya sa har yanzu ba a ga ‘danuwana’ Femi Fani-Kayode a APC ba
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da FFK Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Getty Images

Bello wanda yake mulkin jihar Kogi tun karshen 2015 ya kara da cewa: “Abin da na sani kenan.”

Kwanaki Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fito ya na cewa sun tattauna batun sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode.

An ga gwamnan ya na wannan bayani a wani bidiyo inda ya ke bayyana cigaban da ya samar wa wa jam'iyyar APC mai mulki da sauyin-shekar jagoran hamayyar.

Kwamishinan labaran jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya tabbatar dda ingancin wannan bidiyon.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel