Magajin Buhari: Kungiya ta jadadda goyon bayanta ga Yahaya Bello a 2023

Magajin Buhari: Kungiya ta jadadda goyon bayanta ga Yahaya Bello a 2023

- Kungiya ta nuna goyon bayanta ga shugabancin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a 2023

- A cewar kungiyar Bello shi yafi cancanta ya gaji Shugaban kasa Muhamadu Buhari don ya dora daga inda ya tsaya

- Kungiyar ta bayyana wasu nasarori da gwamnan ya samu yayinda yake jagorantar jihar Kogi

Wata kungiyar magoya bayan shugabancin Yahaya Bello mai suna PYB FRONTIERS ta yi kira ga mutanen Najeriya da su marawa gwamnan baya domin tabbatar da ganin cewa ya gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar, Hans Mohammed a wani jawabi ya ce kungiyar ta fara tattaunawa don tabbatar da ganin gwamnan ya samu tikitin APC, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya bayyana cewa gwamnan ya nuna bajinta a bangarorin tsaro, ilimi mai inganci, fannin lafiya musamman a lokacin annobar korona.

Magajin Buhari: Kungiya ta jadadda goyon bayanta ga Yahaya Bello a 2023
Magajin Buhari: Kungiya ta jadadda goyon bayanta ga Yahaya Bello a 2023 Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da sabbin nade-nade

Mohammed ya bayyana cewa gwamnan ya samu lambar yabo a gida da wajen kasar kan tsaron rayuka da dukiyar al’umman jihar Kogi, cewa bashi wannan babban matsayi zai fi komai dacewa.

“A fannin kula da kudade kadab, gwamnan ya yi namijin kokari. Hakan ya sa ya samu lambar yabo daga hukumar kasafin kudi na jihar tsawon shekaru biyu a jere.

“A bangaren ci gaban harkar noma, Gwamnan ya kuma yi kokari ta hanyar gina kamfanin sashen shinkafa na miliyoyin naira a karamar hukumar Yagba ta Yammacin jihar. Hakan ya samar da ayyukan yi a jihar.

“Duba ku ga hadin kan da ya kawo a tsakanin kabilun da ke Kogi ta hanyar nade naden mukamai da aiwatar da ayyuka a fadin yankunan jihar guda uku. Wannan ne dalilin da yasa muke kira a gareshi da ya fito neman kujerar, domin ya hada kan Najeriya.”

Sun jadadda cewa shugabancin Bello zai kara martaba ga Najeriya da yan Najeriya domin zai ci gaba da dorawa daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya.

Kungiyar ta yanke shawarar yin aiki tukuru wajen tabbatar da ganin cewa Gwamna Yahaya Bello ya zama shugaban kasa a 2023, kamar yadda tayi a zaben gwamnan 2019 a karonsa na biyu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya amince da nadin jakadu 95

A wani labarin kuma, Laori Kwamoti, wani dan majalisan Adamawa mai wakiltan mazabar Numan/Lamurde/Demsa a majalisar wakilai, ya koka kan yadda hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bata masa suna.

Dan majalisan ya bayyana matsayarsa a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, a garin Yola, inda ya kara da cewa hadiman Shugaban kasar sun yi barna sosai a gwamnatinsa.

A cewarsa, furuci mara ma’ana da martanin mafi akasarin masu kula da harkokin labaran Shugaban kasar ya “rage darajar Najeriya zuwa abar dariya.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel