An baiwa Sheikh Gumi lambar yabon Jakadan zaman lafiya a Najeriya

An baiwa Sheikh Gumi lambar yabon Jakadan zaman lafiya a Najeriya

- Sheikh Ahmad Gumi ya samu lambar yabon jakadan zaman lafiya na kasa

- Gumi ya bayyana farin cikinsa da wannan kyauta da ya samu

- Babban malamin ya shahara da shiga daji domin tattaunawa da yan bindiga su ajiye makamai

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Women of Praise And Charity Organization (WPCO) ta baiwa shahrarren Malami, Sheik Ahmad Gumi, lambar yabon Jakadan zaman lafiya na kasa.

Shahrarren Malamin Addinin, Sheikh Ahmad Gumi, ya shahara da kokarin samar da zaman lafiya ta hanyar ayi sulhu da tsagerun yan bindiga.

Gumi ya bayyana cewa yayi matukar farin cikin samun wannan lambar yabo saboda hakan na nuna ana ganin muhimmancin kokarin da yake yi.

"A yau na samu lambar yabon jinjina daga kungiyar ‘Women of Praise And Charity Organization (WPCO)," Gumi yace a shafinsa na Facebook.

"Ina matukar son ire-iren wadannan lambar yabon musamman daga kungiyoyin gida da suka san darajar kokarin samar da zaman lafiyan da nike yi, saboda talaka matsalar tsaro tafi shafa."

KU KARANTA: Matsalar rashin tsaro ta sa Gwamnan Neja zai ba ‘Yan sa-kai manyan bindigogi su shiga jeji

An baiwa Sheikh Gumi lambar yabon Jakadan zaman lafiya a Najeriya
An baiwa Sheikh Gumi lambar yabon Jakadan zaman lafiya a Najeriya Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

DUBA NAN: Ministan Buhari da matarsa sun sabunta rijistar jam'iyyar APC a Rivers

A wani labarin kuwa, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi hukumar Sojin Najeriya martani.

Gumi ya yi raddi ne bayan hukumar Sojin ta gargadesa a wani jawabi da ta saki kan maganar da yayi dake zargin Sojoji Kirista da kashe Fulani masu rike makamai.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook.

A ranar Litinin, Rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen fiaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi, da ya guje zubdawa rundunar mutunci.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel