Ni ma fa Soja ne kuma ina alfahari da hakan, amma akwai batagari cikinku, Gumi ya yiwa hukumar Soji raddi
- Sheikh Abubakar Gumi ya mayar da martani ga hukumar Sojojin Najeriya
- Babban malamin ya shahara da shiga daji domin tattaunawa da yan bindiga su ajiye makamai
- Sojoji sun zargeshi da kokarin kulle kiyayya ta addini tsakanin jami'anta
Shahrarren Malamin Addini mai kokarin samar da zaman lafiya ta hanyar ayi sulhu da tsagerun yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi wa hukumar Sojin Najeriya martani.
Gumi ya yi raddi ne bayan hukumar Sojin ta gargadesa a wani jawabi da ta saki kan maganar da yayi dake zargin Sojoji Kirista da kashe Fulani masu rike makamai.
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook.
A ranar Litinin, Rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen fiaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi, da ya guje zubdawa rundunar mutunci.
Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya janar Mohammed Yerima a wata takarda da ya fitar ya ja kunnen malamin da ya kiyaye yadda zai dinga kwatanta rundunar sojin.
A cewar Gumi, shi ma fa dan gidan Soja ne kuma yana alfahari da hakan amma akwai bata gari cikin wasu hafsoshin hukumar wadanda ke da tsattsaurin ra'ayin addini.
"A matsayina na dan gidan Soja kuma ina alfahari. Lallai kwararru ne. Amma duk da haka tarihi ya nuna wasu laifuka da wasu masu mumunan ra'ayin addini suka aikata na kashe al'umma," Gumi yace.
"Ya kamata hukumar Soji tayi dubi cikin gidanta kuma ta tsarkake kanta daga ire-iren wadannan batagarin dake amfani da makamanta wajen aikata laifuka kan yan Najeriya."
KU KARANTA: Matsalar rashin tsaro ta sa Gwamnan Neja zai ba ‘Yan sa-kai manyan bindigogi su shiga jeji
DUBA NAN: Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da na Buhari, Inji gwamnatin tarayya
A wani labari na daban, ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta soke hukuncinta na sake bude wasu makarantu 10 na jihar inda aka yi rikicin saka hijab.
Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar, Kemi Adeosun ta tabbatar, da farko an bukaci makarantun su bude a ranar Litinin amma an soke hakan.
Ta ce wannan hukuncin an yanke shi ne saboda wasu dalilan tsaro, Premium Times ta wallafa.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng