Matsalar rashin tsaro ta sa Gwamnan Neja zai ba ‘Yan sa-kai manyan bindigogi su shiga jeji

Matsalar rashin tsaro ta sa Gwamnan Neja zai ba ‘Yan sa-kai manyan bindigogi su shiga jeji

- Gwamnan Jihar Neja ya yi alkawarin zai ba ‘Yan sa-kai bindigogi su rike

- Abubakar Bello ya sha alwashin kara wa jami’an sa-kan karfi a jihar Neja

- Jihar Neja ta na ta fama da matsalar kashe-kashe da garkuwa da mutane

Jaridar Daily Trust ta ce Mai girma gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yi alkawarin ba ‘yan sa-kai bindigogi domin su tunkari miyagun ‘yan bindiga.

Da yake magana a Kasuwan Garba, a karamar hukumar Mariga, inda ya gana da jami’an ‘yan sa-kai fiye da 200, gwamnan Nejan ya yi alkawarin zai ba su makamai.

Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce zai raba wa masu kare jama’a bindigogi da nufin su yi maganin ‘makiyan al’umma da ke fadin jihar’, ya na mai nufin ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoninsu a Yankunan Zamfara, Gwamnatin Jiha ta Koka

Gwamna Sani Bello ya kai wannan ziyara zuwa garin Mariga ne domin ya karfafa wa jami’an sa-kai da ke sintiri da tsaron ran mutanen jihar Neja kwarin gwiwa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Yarinyar Ministar Tarayya

Yayin da wasu gwamnoni da mutane su ke kiran ayi sulhu da ‘yan bindiga, gwamna Bello ya hakikance a kan cewa tsakaninsa da miyagun sai dai barin wuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya bayyana cewa ba zai ruguza jami’an tsaron sa-kai ba, asali ma ya sha alwashin zai ba su makamai da nufin su banbaro ‘yan bindiga a duk inda su ke.

“Ba za mu ruguza aikin ‘yan sa-kai saboda barazana daga ‘yan bindiga ba.” Inji gwamna Bello.

Gwamnan ya ce har gobe wadannan jami’ai za su cigaba da aiki; “Ko da an daina ta’adi a jihar, ‘yan sa-kai za su cigaba da aiki na samar da tsaro a kananan hukumomi.”

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu

Matsalar rashin tsaro ta sa Gwamnan Neja zai ba ‘Yan sa-kai manyan bindigogi su shiga jeji
Gwamna Abubakar Sani Bello Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon-gaba da fasinjojin mota a Taraba

Bisa dukkan alamu wannan mataki da gwamnatin Neja ta ke neman dauka zai hada ta fada da hukumomi, domin ‘yan sa-kai ba su da hurumin rike manyan makamai.

A jiya ne ku ka ji cewa tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bernabas Bala Bantex, ya ce masu cin ribar rashin tsaro ba za su so a kawo karshen wannan lamari ba.

Da yake magana da gidan talabijin na Channels Television a shirinsu na siyasa na ‘Sunday Politics’, Bantex ya tattauna halin rashin tsaro da ake fuskanta a kasar.

Bernabas Bala Bantex ya ce ba ya goyon bayan gwamnati ta yi sulhu da Miyagun 'yan bindiga.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel