Ngwuta, alkalin kotun kolin Najeriya ya rasu a garin Abuja

Ngwuta, alkalin kotun kolin Najeriya ya rasu a garin Abuja

- Ubangiji ya karba rayuwar Mai shari'a Sylvester Ngwuta na kotun kolin Najeriya

- Ya rasu bayan rashin lafiya da yayi har ya kwanta a asibitin kasa dake babban birnin tarayya

- Rashin lafiyar ya tsananta a ranar Juma'a 5 ga watan Maris amma ya rasu a ranar Lahadi

Mai shari'a Sylvester Ngwuta na kotun kolin Najeriya ya rasu. Majiyoyi daga kotun kolin sun tabbatar da cewa ya rasu ne wurin karfe 2 na safiyar Lahadi.

An gano cewa Ngwuta yana shirin yin murabus a ranar 30 ga watan Maris 2021 domin zai cika shekaru 70 a duniya, Daily Trust ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi, babban rijistra ta kotun, Hadizatu Uwani Mustapha, tace mai shari'a Ngwuta ya kwanta a asibitin kasa dake Abuja inda ya kwashe mako daya.

KU KARANTA: Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki

Ngwuta, alkalin kotun kolin Najeriya ya rasu a garin Abuja
Ngwuta, alkalin kotun kolin Najeriya ya rasu a garin Abuja. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Ta kara da cewa kafin a mayar dashi sashin kula na musamman (ICU) na asibiti a ranar Juma'a, 5 ga watan Maris, an gano baya dauke da cutar korona.

"An adana gawar shi a wurin adana gawawwaki na asibitin kasa dake Abuja kafin a shirya bikin birne shi," takardar tace.

“Muna fatan Mai shari'a Sylvester Ngwuta na kwance cikin aminci kuma Ubangiji ya ba iyalansa dangana da dukkan ma'aikatar shari'a na wannan babban rashin."

KU KARANTA: Ku daina tsokacin da zai zama kalubale ga tsaron kasa, Ganduje ga 'yan siyasa

A wani labari na daban, zakakuran sojin Najeriya sun sheke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan bindiga ne karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a Katsina, The Cable ta wallafa.

Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a ranar Alhamis a kauyen Marina dake karamar hukumar Safana ta jihar.

Akasin rahotannin da ke yawo na cewa an halaka sojoji masu yawa a yankin, Mohammed Yerima, kakakin rundunar sojin a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, yace soja daya ne ya rasa rayuwarsa a yayin musayar wutar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel