Da duminsa: Gwamnatin Kwara ta sake garkame makarantu 10 a kan rikicin Hijab

Da duminsa: Gwamnatin Kwara ta sake garkame makarantu 10 a kan rikicin Hijab

- Ma'aikatar ilimin jihar Kwara ta sake garkame makarantu 10 da ta ba damar budewa

- Gwamnatin jihar tace ta yi hakan ne saboda lamurran tsaro sakamakon rikicin hijab da aka yi

- Kamar yadda sakatariyar ma'aikatar ilimin ta sanar, an bukaci daliban da malaman su zauna gida

Ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta soke hukuncinta na sake bude wasu makarantu 10 na jihar inda aka yi rikicin saka hijab.

Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar, Kemi Adeosun ta tabbatar, da farko an bukaci makarantun su bude a ranar Litinin amma an soke hakan.

Ta ce wannan hukuncin an yanke shi ne saboda wasu dalilan tsaro, Premium Times ta wallafa.

"A don haka gwamnatin take umartar 'yan makarantun da malamansu da su zauna a gida akasin sanarwar farko da aka yi.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock

Da duminsa: Gwamnatin Kwara ta sake garkame makarantu 10 a kan rikicin Hijab
Da duminsa: Gwamnatin Kwara ta sake garkame makarantu 10 a kan rikicin Hijab. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

“Gwamnatin ta mayar da hankali wurin adalci da mutunta doka da hakkokin dukkan 'yan kasa a kowanne lokaci," takardar tace.

A watan Fabrairu ne gwamnatin jihar ta bukaci da a rufe wasu makarantu 10 na jihar dake Ilorin har zuwa lokacin da za a shawo kan rikicin saka hijab.

Makarantun sune: C&S College, ST. Anthony College, ECWA School, Surulere Baptist Secondary School, Bishop Smith Secondary School, CAC Secondary School, St. Barnabas Secondary School, St. John School, St. Williams Secondary School da St. James Secondary School.

KU KARANTA: Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki

A wani labari na daban, a ranar Lahadi ne sojojin Najeriya suka hana mayakan Boko Haram daga mamaye babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Borno.

An gano cewa sojojin sun yi musayar wuta tsakaninsu da 'yan Boko Haram a garin Mainok da Jakana.

Wani matukin motar haya ya sanar da Daily Trust cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan an bude titin da aka saba rufewa duk yammaci. Sojojin suna rufe babbar hanyar duk yammaci kuma su budeta da karfe 7 na safiyar kowacce rana.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel