Hotuna da bidiyon gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi, Bishi Taiwo, da NDLEA ta kama
- Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta damke wani gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi
- An kama Hassan Bishi Taiwo a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Mohammed dake Legas
- An kama shi da sinkin hodar iblis uku wanda za a tura kasashen Amurka, Dubai da kuma China
Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa ta cafke gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi da sunki uku na hodar ibilis a filin sauka da tashin jiragen sama na Legas.
An shirya miyagun kwayoyin ne domin aika su ga Amurka, China da Dubai. An kara da samo wasu sunkin hodar ibilis da aka boye a fadar basarake.
KU KARANTA: Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya
Wanda ake zargin mai suna Hassan Bishi Taiwo an kama shi sakamakon binciken jami'an hukumar NDLEA a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Mohammed dake Lagos.
Karin bayani na nan tafe...
KU KARANTA: Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo
A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta tabbatar da tashin gobara a farfajiyar fadar shugaban kasa dake Aso Rock.
Kamar yadda Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasan ya sanar, lamarin ya faru ne tsakanin fadar da barikin sojoji kusa da hanyar Asokoro.
Ya musanta rade-radin da ake fadi na cewa gobarar a cikin fadar shugaban kasar ta tashi, The Cable ta wallafa. A wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, Shehu yace wutar daji ce kuma ana cigaba da bincike a kan lamarin.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng