Gwamnatin Katsina za ta mayar da Almajirai 7,893 jihohinsu ciki har da ƴan Nijar

Gwamnatin Katsina za ta mayar da Almajirai 7,893 jihohinsu ciki har da ƴan Nijar

- Gwamnatin Jihar Katsina za ta mayar da Almajirai 7,893 jihohinsu na haihuwa

- Kimanin guda 2,052 cikin Almajiran yan kasar Jamhuriyyar Nijar ne

- Kwamishinan muhalli na jihar Katsina, Hamza Faskari ne ya sanar da hakan

- Faskari ya kuma bayyana cewa gwamnatin za ta yi wa tsarin makarantun allo garambawul

Gwamnatin jihar Katsina za ta mayar da Almajirai 7,893 zuwa jihohinsu na ainihi da ƙasashen su. Guda 2,052 cikin Almajiran ƴan Jamhuriyar Nijar ne, a cewar rahoton na The Punch.

Kwamishinan muhalli na jihar, Mallam Hamza Faskari ne ya shaidawa manema labarai hakan a yammacin ranar Laraba bayan taron Kwamitin Zartarwa na Jihar da Gwamna Aminu Masari ya jagoranta.

DUBA WANNAN: Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji

Gwamnatin Katsina za ta mayar da Almajirai 7,893 jihohinsu ciki har da ƴan Nijar
Gwamnatin Katsina za ta mayar da Almajirai 7,893 jihohinsu ciki har da ƴan Nijar. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Bai bayyana ranar da za a fara mayar da Almajiran garuruwan su ba.

Ya ce, "Kwamitin Zartarwa na Jihar Katsina ta amince da mayar da Almajirai 7,893 da aka gano ba ƴan jiha bane zuwa ainihin jihohinsu har da Jamhuriyar Nijar".

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

Kwamishinan ya kuma yi magana kan shirin garambawul da za a yi wa tsarin makarantun allo a jihar.

Ya ce kwamitin ta amince da fitar da N3,365,709.846 domin magance ambaliyar ruwa a jihar.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel