Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa hukumomin tsaro umurnin bindige duk wanda suka kama da AK-47
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da aka yi da shi
- Shehu ya ce Shugaba Buhari ya bada umurnin ne domin kawar da yan bindiga, masu garkuwa da sauran bata gari da suka ki mika wuya
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaro da su harbi duk wani da suka gani dauke da bindigar AK-47.
Shehu ya bayyana hakan ne cikin wata hira da BBC ta yi da shi, ya ce shugaban kasar ya bada umurnin a kawar da yan bindigan da suka ki mika wuya su ajiye makamai.
DUBA WANNAN: Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi
A watan Nuwamba, Alhaji Sa'ad Abubakar, Sarkin Musulmi ya ce yan bindga suna yawo dauke da AK47 a sassa daban-daban na arewacin kasar.
A kokarin samar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara da wasu jihohin arewa, Shehu ya ce gwamnati za ta yi amfani da karfin bindiga kan wadanda suka ki su mika wuya.
"Shugaban kasar ya umurci jami'an tsaro su shiga dazuka su bindige wanda suka gani dauke da muggan makamai kamar AK-47," ya ce a hirar da aka yi da shi.
KU KARANTA: 2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugaban ƙasa'
"Ya bada umurnin a harbe duk wani da aka gani da muggan makamai nan take."
Har wa yau, kakakin shugaban kasar ya kuma ce gwamnatin tarayya ta kafa dokar hanawa jirage keta sararin samaniyar jihar Zamfara ne bayan ya samu bayanin sirri da ke nuna cewa ana kai wa yan bindiga makamai ta hanyar amfani da jirage na masu zaman kansu.
Ya kuma ce ana amfani da jiragen ana tafiya da gwala-gwalai zuwa Dubai, hakan yasa shugaban kasar ya bada umurnin a dakatar da hakkar gwala-gwalan.
A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.
NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng