Abdul-Jabbar: JNI ta ce ba za ta hallarci muqalabar da gwamnatin Kano ta shirya ba

Abdul-Jabbar: JNI ta ce ba za ta hallarci muqalabar da gwamnatin Kano ta shirya ba

- Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabalar da gwamnatin Kano ta shirya tsakanin Abdul-Jabbar da malaman Kano ba

- Kungiyar ta musulunci ta ce ba a tuntube ta ba yayin shirya mukabalar da tun farko take ganin bai ma dace a yi ba ba da wanda ke yi wa Annabi (SAW) batanci

- JNI ta ce bisa koyarwar mafi yawancin malaman fiqihu babu bukatar a bawa wanda ke yi wa Annabi (SAW) batanci damar kara watsa mummunar akidarsa

Kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

Jama’atu Nasril Islam ta ce ba za ta hallarci mukabala da Sheikh Abduljabbar ba
Jama’atu Nasril Islam ta ce ba za ta hallarci mukabala da Sheikh Abduljabbar ba. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

JNI, ta Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar.

Ta kuma soki 'kalaman batanci' da ake yi ga Manzon Allah da iyalansa da sahabansa cikin wata sanarwa da sakatarenta Khalid Aliyu ya fitar.

"Da farkon lamarin, mun yabawa gwamnatin Kano kan matakin da ta dauka na dakile fitina a kasa da rushewar doka," in ji shi.

"Mun kuma sa ran gwamnatin za ta tuntubi mutane da dama kan batun tunda lamari ne da ya shafi kasa baki ko duniya baki daya ba jihar Kano ba."

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutane 60 bayan kona gidaje a Ruwan Tofa a Zamfara

Kungiyar Jama'atu ta ce bai dace gwamnati da jama'a su bawa Abdul-Jabbar muhimmanci ba duba da abin Allah wadai da ya aikata na batanci da Annabi Muhammadu (SAW).

"Bisa koyarwar mafi yawancin malaman fiqihu, JNI na ganin bai ma dace a yi mukabala da Abdu-Jabbar ba duba da cewa yana yi wa Annabi (SAW) batanci a fili. An san matsayinsa a musulunci; babu bukatar sake bashi dama watsa batancinsa ga duniya.

"Idan da gwamnatin Kano ta tuntubi manyan mutanen da ya kamata domin shirya mukabalar, da an kaucewa fada wa matsalar da aka shiga a yanzu. Don haka, JNI ta ce ba a tuntube ta ba kan matakan da ake dauka kawo yanzu don haka ba za ta hallarci mukabalar ba kuma babu wani sashinta da zai hallarta."

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel