Kuma dai: Lambar tsohon Shugaban EFCC, Magu, ta fito a zargin da ake yi wa Maina a kotu

Kuma dai: Lambar tsohon Shugaban EFCC, Magu, ta fito a zargin da ake yi wa Maina a kotu

- Ngozika Ihuoma ya bada shaida a shari’ar da ake yi da Mr. Abdulrasheed Maina

- Ihuoma ya fadi yadda EFCC ta karbe wasu kadarori daga hannun PRTT a baya

- Ibrahim Magu bai sanar da Majalisa cewa EFCC ta karbe wadannan dukiya ba

Daily Trust ta ce Ngozika Ihuoma, wanda ya bada shaida a kotu a ranar Alhamis, ya jefa tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu, a badakalar Abdulrasheed Maina.

Ana shari’a a kotu inda ake zargin tsohon shugaban kwamitin binciken kudin fansho (PRTT), Abdulrasheed Maina da zargin yin sama da fadi da dukiyar al’umma.

Ngozika Ihuoma ya sanar da Alkalin kotu, Okon Abang, yadda wani jami’in EFCC ya mallaki wani gida da ake bincike a kai, yayin da ake tsakiyar zaman shari’ar a kotu.

Wanda ya bada shaidan ya nemi a EFCC ta fito da kadarori 222, daga ciki har da wani katafaren gidan Biliyan 6 da aka saida wa Lauyan na EFCC a kan Biliyan 1 rak.

KU KARANTA: Laifuffukan da ake zargin Magu da aikatawa a EFCC

Ihuoma ya ce a lokacin da Magu ya bayyana a gaban majalisar wakilai a kan binciken dawo da Maina bakin aiki, ya musanya cewa PRTT ta na tare da hukumar EFCC.

Sannan shaidan ya bayyana cewa Magu ya yi ikirarin PRTT ba ta mallaka wa EFCC wasu kadarori ba.

A dalilin hakan, wannan mutumi da yake bada shaida ya sanar da kotu cewa Ibrahim Magu ya yi karya, ya kuma karya rantsuwar da a yi a binciken Maina da aka yi.

Lauyan da ta ya tsaya wa tsohon shugaban PRTT da aka ruguza, Olawale, ya shaida wa kotu yadda Maina ya fada wa gwamnati hanyar da za ta karbo Naira tiriliyan 3.

KU KARANTA: Yadda Maina su ka sace kudin fansho - EFCC

Kuma dai: Lambar tsohon Shugaban EFCC, Magu, ta fito a zargin da ake yi wa Maina a kotu
Ibrahim Magu Hoto: EFCC
Asali: UGC

Adeola Olawale ya ce a 2016 Maina ya hadu da NSA da AGF a Dubai, ya yi masu bayanin yadda za a bi a karbo N1.3tr daga cikin N3tr da aka wawura daga baitul-mali.

Kwanakin baya ne Jami'an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci su ka kama Abdulrasheed Maina a Nijar, bayan ya sulale daga Najeriya.

An samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami'an Najeriya da Nijar.

Da ake zaman kotu, Abdulrasheed Maina ya ce bai aikata laifin komai ba duk da cewa hukumar EFCC ta na yi masa tuhuma 12, kuma ya tsere bayan ya samu beli.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel