Da duminsa: An kama Abdulrasheed Maina a Nijar

Da duminsa: An kama Abdulrasheed Maina a Nijar

- Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, ya matsa layar zana a yayin da kotu ke nemansa a Najeriya

- Bacewar maina ta sa kotu ta tsare Sanata Ali Ndume a gidan yari saboda shine ya karbi belin Maina bisa wasu sharudai

- Yanzu dai, karya ta kare, jami'an tsaro ma su bincike tare da hadun gwuiwar jami'an yaki da cin hanci sun sake cukume Maina a Nijar

Jami'an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar.

A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami'an tsaron Najeriya da Nijar.

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ne ta sanar da janye belin Abdulrasheed Maina tare da bayar da umarin a kama shi duk inda aka gan shi.

KARANTA: EFCC ta sake gurfanar da Babachir a gaban sabon alkali a kan kwangilar cire shu'umar ciyawa a N544m

A hukuncin da alkalin kotun, Okong Abang, ya zartar ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, ya bayar da umarnin a sake kamo Maina ''duk inda aka gan shi".

Da duminsa: An kama Abdulrasheed Maina a Nijar
Da duminsa: An kama Abdulrasheed Maina a Nijar
Asali: UGC

Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce an bayar da belin Maina a kan kudi miliyan N500 da kuma mai tsaya masa; wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye miliyan N500 a kotu.

Lauyan ya rubuta takardar korafi zuwa kotun inda a ciki ya zargi Maina da saba sharuda da ka'idojin belin.

KARANTA: Kaduna: An shafe tsawon dare ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Jaji

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhuma goma sha biyu da ta shirya a kansa da kuma wani kamfani mai suna 'Common Input Properties & Investment Limited".

Bayan bawa hukumomin tsaro izinin kama shi, kotun ta bawa EFCC damar gurfanar da shi tare da tuhumarsa a kebance.

Kafin Sanata Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe tsawon watanni bakwai a gidan yarin Kuje.

Bayan Maina ya cika bujensa da iska, kotu ta bayar da umarenin tsare Sanata Ndume a gidan yari na Kuje.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa an hana wasu sanatoci damar ganin Ndume a gidan gyaran halin Kuje da ke Abuja.

An garkame Ndume ne a maimakon Maina, tsohon shugaban hukumar fansho da ake tuhuma da laifin wawura da sama da fadi da kudaden jama'a.

Da Sanata Na'Allah yaje ganin Ndume a gidsan gyarean hali, ya ce bai taba ganin irin wannan wulakancin ba a rayuwarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel