Sadiq Daba: Tsohon ɗan jarida kuma ɗan wasan kwaikwayo ya rasu

Sadiq Daba: Tsohon ɗan jarida kuma ɗan wasan kwaikwayo ya rasu

- Allah ya yi wa tsohon dan jarida kuma dan wasan kwaikwayo, Sadiq Daba rasuwa

- Daba ya rasu a daren ranar Laraba 3 ga watan Maris a gidansa da ke Legas misalin karfe 8.30 na dare

- Daba na daga cikin taurarin yan jarida da yan wasan kwaikwayo da suka yi fice tun shekarun 1980s

Tsohon jarumin Nollywood kuma kwararren dan jarida Sadiq Daba ya rasu. An ce tsohon dan jaridar ya rasu ne a ranar Laraba 3 ga watan Maris misalin karfe 8.30 na dare a gidan da ke Legas.

Sadiq ya rasu bayan ya dade yana fama da kansa ta Leukemia da Prostrate kamar yadda Channels Television ta ruwaito.

Sadiq Daba: Tsohon dan jarida kuma dan wasan kwaikwayo ya rasu
Sadiq Daba: Tsohon dan jarida kuma dan wasan kwaikwayo ya rasu. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

Mai hada fina-finai, Kunle Afolayan wanda ya yi aiki da Sadiq a baya-bayan nan a fim mai suna 'Citation' ya tabbatar da rasuwarsa.

Afolayan ya ce ya yi magana da matarsa da dansa sun kuma tabbatar masa da rasuwarsa.

Yan Nigeria da dama ciki har da attajiri Femi Odetola son tallafa masa da kudi domin ya fita kasar waje a yi masa magani.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Daba ya yi fice sosai a shekarun 1980 lokacin da ya ke aiki da Hukumar Talabijin na Kasa, NTA.

Ya fito a fina-finai da wasannin kwaikwayo da dama ciki har da ‘Cockk Crow at Dawn’ da ‘October 1st’ da suka fi fice.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel