Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto

Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto

- Hukumar NDLEA ta yi nasarar cafke wani da ake zargi mai safarar miyagun kwayoyi ne da hodar Ibliss mai nauyin 1.550kg

- Hukumar ta ce an kama wani Nkem Timothy ne amma an same shi da fasfo mai dauke da sunan Auwalu Audu yana kokarin ketare bodar Illela

- Hukumar ta ce bata taba kama hodar iblis mai yawan wannan ba a Sokoto kuma ta fara bicike don gano masu daukar nauyinsa da sauran abokansa

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg.

Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto
Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Babafemi ya ce ya jiyo kwamandan NDLEA a Sokoto, Bamidele Segun, yana cewa an kama wanda ake zargin a kan babur kusa da Baggage a bodar Illela yayin da ya ke kokarin shiga Jamhuriyar Nijar kafin ya karasa Aljeriya inda ya ke zama.

KU KARANTA: Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna

Ya ce an boye miyagun kwayoyin a cikin kwallaben madarar yogurt.

"An same shi da fasfo na ECOWAS mai dauke da suna daban, Auwalu Audu, amma ya ce asalin sunansa Nkem Timothy," in ji kwamandan.

Ya ce hukumar ta fara zurfafa bincike domin gano masu daukar nauyinsa da sauran mambobin kungiyarsa da ke safarar tare da shi.

"Wannan babban kamu ne duba da adadin hodar iblis din da muka samu, ba a taba samun irinsa a nan Sokoto ba."

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel