Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

- Allah ya yi wa wani ango mai suna Adamu rasuwa kwana daya bayan daurin aurensa

- Kamar yadda abokansa suka wallafa a dandalin sada zumunta, sunce mutuwar kawai ta zo ne nan take

- Mutane da dama sun yi masa addu'ar Allah ya jikansa ya bawa matarsa da iyalansa hakurin jure rashinsa

Wani matashi dan Nigeria mai suna Ango Adamu ya riga mu gidan gaskiya kwana daya bayan daura aurensa a garin Matumbi a jihar Neja.

An gano cewa marigayin da aka daura masa aure tare da amaryarsa a ranar Juma'a 26 ga watan Fabrairun 2021 a garin Matumbi a Neja ya rasu a ranar Asabar 27 ga watan Fabrairu.

Allah ya yi wa ango rasuwa kwana daya bayan daurin aurensa
Allah ya yi wa ango rasuwa kwana daya bayan daurin aurensa. Hoto: Usman Moh'd Ciroma
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugaban ƙasa'

A cewar daya daga cikin abokansa mai suna Usman Mohd Chiroma, mutuwar ta zo ne "nan take".

Allah ya yi wa ango rasuwa kwana daya bayan daurin aurensa
Allah ya yi wa ango rasuwa kwana daya bayan daurin aurensa. Hoto: Usman Moh'd Ciroma
Asali: Facebook

"Tabbas, mutuwa abu ne mai katse duk ni'imomi. Hoton farko shine fuskar marigayi Adamu da kyakyawar amaryarsa, ya rasu kwana daya bayan daura masa aure. Hoton na biyu kuma an dauka ne a lokacin yi masa jana'iza," Chiroma ya rubuta a ranar Litinin 1 ga watan Maris.

"Allah yasa Aljannah ce makomarsa kuma ya bawa amaryarsa da daukakin iyalanta hakurin jure wannan rashin"

KU KARANTA: Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi

Wasu abokansa da yan uwa da abokan arziki sun yi masa addu'o'in Allah ya jikansa ya yafe masa kurakurensa inda suma suka wallafa hotunansa.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel