Yanzu-yanzu: An bindige jami'an 'yan sanda har lahira a Cross Rivers

Yanzu-yanzu: An bindige jami'an 'yan sanda har lahira a Cross Rivers

- Bata gari sun kai wa yan sanda hari sun halaka a kalla biyu a jihar Cross Rivers

- Mai magana da yawun yan sandan jihar Cross Rivers, Irene Ugbo ta tabbatar da hakan

- Ugbo ta kuma kara da cewa bata garin da suka halaka yan sandan sun tsere da bindigunsu

A kalla yan sanda biyu ne aka kashe a karamar hukumar Obubra da ke jihar Cross River, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyoyi daga garin, wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka bindige yan sandan a safiyar ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Kuma dai, Ƴan bindiga sun sace ɗalibai 3 a jihar Katsina

Yanzu-yanzu: An bindige jami'an 'yan sanda har lahira a Cross Rivers
Yanzu-yanzu: An bindige jami'an 'yan sanda har lahira a Cross Rivers. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Irene Ugbo, mai magana da yawun yan sandan jihar Cross Rivers ta tabbatar wa jaridar Daily Trust afkuwar lamarin.

Ugbo, wadda ba ta bata cikakken bayani kan afkuwar lamarin ba ta ce sun dauke bindigun yan sandan da suka kashe.

A wani labarin mai kama da wannan an ruwaito cewa an kashe wani soja yayin harin da aka kai amma Daily Trust bata iya tabbatar da rahoton ba.

A kalla yan sanda 10 ne aka kashe su a bakin aikinsu cikin mako daya.

KU KARANTA: An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja

A makon da ta gabata, yan bindiga sun afka ofishin yan sanda a jihohin Imo da Abia sun kashe jami'ai sun kona ofishohin.

Kakakin yan sanda na kasa, Frank Mba, daga bisani ya sanar da cewa an kashe wasu daga cikin wadanda suka kai harin a Aba, jihar Abia.

A maimakon hakan ya zama darasi ga masu kai harin, suna sake kai sabbin hare-hare musamma a kudu.

Kawo yanzu ba a san manufarsu ba.

Rabon ta a kai wa yan sanda irin wannan harin dun lokacin zanga-zabagr Endsars a watan Oktoban 2020.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel