Kuma dai, Ƴan bindiga sun sace ɗalibai 3 a jihar Katsina
- 'Yan bindiga sun sake dace daliban makarantar sakandare su uku a Katsina
- An sace daliban su maza uku ne daga Community Day Secondary School a Gobirawa
- An yi kokarin ji ta bakin ma'aikatar ilimi na jihar da yan sanda amma abin ya ci tura
An sace dalibai guda uku daga kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina a ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wani mazaunin Gobirawa wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatarwa Daily Trust cewa an sace daliban ne bayan an tashe su daga makaranta a Community Day Secondary School a Gobirawa.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue
"Ba makarantar kwana bace kuma dukkan daliban uku da aka sace maza ne kuma suna hanyar komawa gidansu ne da rana bayan an tashi makaranta," a cewar majiyar.
Majiyar ta kara da cewa ana ganin kamar cewa gwamnatin jihar ta bada umurnin rufe makarantar bayan afkuwar lamarin.
An yi kokarin ji ta bakin jami'an makarantar amma hakan bai yiwu ba domin kwamishinan Ilimi na jihar, Dr Lawal Badamasi bai amsa kirar da aka masa a waya ba.
Shi kuma mai magana da yawun ma'aikatar ilimin jihar Katsina, Sani Danjuma ya ce bai da labarin afkuwar lamarin domin baya jihar ya yi balaguro domin yin wani aiki.
KU KARANTA: Cacar-baki kan AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu
Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce zai kira ofishin DPO na karamar hukumar Safana domin tabbatar da sahihancin rahoton.
A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.
NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng