An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja

An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja

- Yan bindiga sun sake sace fasinjoji a kalla 50 a hanyar Tegina zuwa Minna a jihar Neja

- Yan bindigan sun tare titi ne sannan suka kama motocci uku suka tisa keyar fasinjojin da direbobin

- Wani babban jami'in gwamnati a jihar wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da afkuwar lamarin

- Amma an yi kokarin tuntubar kakakin yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, amma bai daga wayarsa ba

A kalla fasinjoji 50 ne yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Talata a kan hanyar Tegina zuwa Minna a karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, yan bindigan sun tare titi a garin Kundu da ke kusa da garin Zungeru suka kama motoccin fasinjoji uku har da direbobin motoccin.

An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja
An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Sun tisa keyar fasinjojin motoccin uku zuwa cikin daji yayin da suka bar motoccin a kan titi.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue

A wani lamari mai kama da wannan, yan bindiga sun sace mutane da ba a tabbatar da adadinsu ba daga kauyen Gidigori da ke karamar hukumar Rafi, sun kona motocci biyar sun kuma sace kayayyaki.

Da ya ke tabbatar da wannan, wani babban jami'in gwamnati da ya nemi a boye sunansa ya ce har yanzu ba a ji komai daga yan bindigan ba ballantana jami'an tsaro su san wadanda aka sace.

Kazalika, an halaka mutum daya an kuma yi garkuwa da wasu da dama yayin da yan bindiga suka afka garin Manta da ke karamar hukumar Shiroro a yammacin ranar Litinin.

KU KARANTA: Cacar-baki kan AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu

Yan bindigan sun sace kayan abinci daga gidajen mutane da wasu kayayyakin.

An yi kokrin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, Wasiu Abiodun amma bai daga wayarsa ba.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel