Cacar-baki kan AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu

Cacar-baki kan AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu

- Gwamnonin jihohin Bauchi da Benue sun yi sulhu bayan cacar baki kan rike AK-47 da makiyaya ke yi a sassan NigeriA

- Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya ce bai ga laifin makiyaya ba da ke yawo da bindiga don kare kansu

- Takwararsa Samuel Ortom kuma ya zargi Bala Mohammed da goyon bayan ta'addanci saboda ya ce bai ga laifin makiyayi da rika yawo da bindiga ba

- Har ta kai da Ortom ya yi zargin cewa wasu nA barazana ga rayuwarsa kuma idan wani abu ya faru da shi a kama Gwamna Bala Mohammed

Gwamnan Benue, Samuel Ortom da takwararsa Mohammed Bala na jihar Bauchi sun rungumi juna bayan yin sulhu a ranar 2 ga watan Maris a jihar Rivers, The Nation ta ruwaito.

Gwamnonin biyu sun yi sulhu kan maganganun da suka rika jefa wa juna game da Ak-47 a yayin da ake fama da rashin tsaro a kasar.

AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu
AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Mohammed, a ranar 1 ga watan Fabrairu ya ce makiyaya ba su da zaɓi shi yasa suke yawo da Ak-47 don kare kansu da shanunsu daga ƴan fashi.

DUBA WANNAN: Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin

AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu
AK-47: Hotunan gwamnonin Bauchi da Benue sun rungumi juna bayan sulhu. @TheNationNews
Asali: Twitter

Ya kuma soki gwammonin johohin kudu maso yamma, Kudu maso gabas, da Gwamna Ortom kan yadda suke tafiyar da rikicin makiyaya da manoma.

Ortom a ranar 22 ga watan Fabrairu ya mayarwa takwararsa na Bauchi martani inda ya zarge shi da ta'addanci saboda yana goyon bayan makiyaya su rika yawo da Ak-47 don kare kansu.

Ortom ya kuma yi zargin cewa gwamnan Bauchi na cikin waɗanda ke barazana ga rayuwarsa kuma a kama shi idan wani abu ya faru da shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe

Bayan musayar kalaman gwamnonin jam'iyyar su na PDP sun saka baki don sulhunta su.

Gwamnan Rivers Nyesome Wike da takwararsa na jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ne suka fara sulhun.

Sulhun su ya yi tasiri a ranar Talata inda Gwamna Ortom da Mohammed suka rungumi juna a Rivers.

Bayan taron sirri a gidan Wike da Port Harcourt, gwamnonin biyu sun ce musayar kalaman da suka yi game da ɗaukan makamai da makiyaya ke yi don cigaban ƙasa ne ba tada yaƙin ƙabilanci ba.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164