Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Terkula Suswam, yayan tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam

- Lamarin ya faru ne misalin karfe 8.46 na daren ranar Talata 2 g watan Maris na shekarar 2021

- Wani shaidan ganin ido ya ce makasan sun zo cikin mota kirar Toyota ne suka harbe Terkula da hadiminsa a kofar gida

'Yan bindiga sun halaka Terkula Suswam, yayan tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam a jihar Benue, The Nation ta ruwaito.

An kashe shi ne tare da hadiminsa a garin Anyiin, Gaambetiev a karamar hukumar Logo da ke jihar Benue.

DUBA WANNAN: Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne misalin karfe 8.46 na daren ranar Talata kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Wani shaidan ganin ido, wanda ya nemi a boye sunansa ya shaidawa The Nation cewa marigayi Suswam yana wasu kananan ayyuka ne a kofar gidansa sai wata mota Toyota ta bullo.

KU KARANTA: 2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugaban ƙasa'

Shaidan ganin idon ya ce Suswam din ya zargi motar don haka ya juya zai shiga gida amma suka bindige shi nan take.

Yan bindigan sun kuma halaka hadiminsa wanda ya ke tare da shi a kofar gidan.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164