Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin

Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin

- Mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace garin Dikwa bayan cin galaba kan sojoji a Borno

- Tun da daren jiya Litinin ne sojoji suka fatattaki yan ta'addan amma suka sake shiri suka dawo

- Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewa yan ta'adda sun karbe garin suna bi layi-layi suna shella

Sojoji a daren ranar Litinin sun dakile hain da yan ta'addan suka kai garin na Dikwa, amma yan ta'addan sun sake dawowa bayan wasu awanni sun ci galaba a kan sojojin, rahoton Daily Trust.

Mazauna garin sun ce yan ta'addan sun yawo cikin gari suna yi wa mutane wa'azi cewa kada su bar garin.

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram suna taruwa a jiha ta, in ji Gwamnan Nasarawa

Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin
Yanzun nan: 'Yan Boko Haram sun ƙwace Dikwa da dubban mutane cikin garin. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ana fadawa mutanen gari cewa yan ta'addan suna tare da su, kamar yadda majiya daga Maiduguri ta bayyana.

Hakan na zuwa ne bayan an karo jami'an tsaro su kwace garin na Dikwa.

Bukar, Ahmed, mazaunin Dikwa, ya zubda hawaye a yayin da ya ke bayyana yadda yan ta'addan suka fadawa makwabcinsa ya zauna.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe

"Sun ce mu tsaya," ba ku muka zo mu taba ba, da sojoji muke yaki." Sun iso garin da baburansu da da motocci masu bindiga.

"Yanzu da muke magana Boko Haram sun kwace garin Dikwa, suna yawo a cikin gari, ku taimake mu ku roki Shugaba Buhari ya cece mu," ya ce, yana kuka a wayar tarho.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel