'Yan Boko Haram suna taruwa a jiha ta, in ji Gwamnan Nasarawa

'Yan Boko Haram suna taruwa a jiha ta, in ji Gwamnan Nasarawa

- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce yan ta'adda sun mayar jiharsa sabuwar matattarsu

- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a jiharsa da aka yi a gidan gwamnati da ke Lafia

- Gwamnan ya ce satar dalibai da ya faru a wasu jihohin kasar nan ya saka gwamnatinsa ta dauki sabbin matakan inganta tsaro

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa mambobin Darul Salam, tsagi na Boko Haram sun mayar da jiharsa matattararsu, News Wire ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne yayin taro da wasu masu ruwa a tsaki ciki har da masu sarautun gargajiya daga kananan hukumomi buyar da abin ya shafa a gidan gwamnati da ke Lafia a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Tawagar gwamnan Bauchi ta yi haɗari, 'yan sanda 10 sun jikkata

'Yan bangaren Darul Salam na Boko Haram suna taruwa a jiha ta, Gwamnan Nasarawa
'Yan bangaren Darul Salam na Boko Haram suna taruwa a jiha ta, Gwamnan Nasarawa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

A cewarsa, da dama cikin, "mambobin Darul Salam, wadanda suka tsinke daga Boko Haram a yanzu suna haduwa a kananan hukumomi 5 cikin 13 na jiharsa.

"Kananan hukumomin sune: Nasarawa, Awe, Doma, Wamba da Karu. Hakan ya tada hankulan jama'ar jihar don hakan ya haifar da sabbin hare-hare bayan jami'an tsaro sun fatattake su a baya bayan nan."

KU KARANTA: Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto

Ya ce rahotannin tsaro ya saka gwamnatinsa daukar matakan tsaro don kare lafiya da dukiyoyin jama'ar jiharsa.

Gwamna Sule ya ce satar dalibai da aka yi a makarantu a wasu jihohi ya saka an inganta sintirin jami'an tsaro a kusa da makarantun kwana na mata a Wamba, Garaku, Udege da Panda.

Gwamnan ya ce rikici a wasu jihohin Kudu maso yamma ya kara janyo tabarbarewar lamarin tsaro saboda shigowar wasu mutane da ba a san inda suka fito ba zuwa kananan hukumomin Awe, Karu, Wamba da Doma.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164