'Yan bindiga sun yi barazanar kashe mu, su soya namar mu su cinye, Ɗalibar Jangebe
- Daya daga cikin daliban da aka ceto daga makarantar mata ta Jangebe, ta magantu kan halin da suka shiga
- Dalibar, mai suna Hafsat Anka, ta ce yan bindigan sun yi barazanar za su kashe su sannan su soya namansu su cinye
- Hafsat ta ce sun sha tafiya mai tsawo a kafa, sannan babu isashen abinci ko ruwa mai tsafta, sai dai razana su da bindiga
Ɗaya daga cikin daliban makarantar sakandare ta mata na Jangeɓe da aka sace makon da ya gabata, Hafsat Anka, ta ce masu garkuwar sunyi barazanar za su kashe su, su soya su sannan su cinye su idan suka yi rashin ji, News Wire ta ruwaito.
Hafsat, yayin da ta ke bayyana wa kamfanin Dilancin Labarai NAN halin da suka shiga ta ce sun yi tafiya na awanni bayan sace su kafin su kai wurin da aka ajiye su.
DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram suna taruwa a jiha ta, in ji Gwamnan Nasarawa
Ta magantu ne a gidan gwamnati da ke Gusau bayan an sako su kamar yadda News Wire ta ruwaito.
"Babu ruwa mai tsafta ko abinci, gani muke kamar shekaru muka shafe bayan kwana ɗaya da sace mu kuma ƴan bindigan suna ta harba bindiga sama domin su firgita mu.
"Matasa ne sai wani babban su da suke kira Kasalle ko Yaya wanda shine ke ba su umurni, kuma shine ya ce kada kowa ya taɓa mu a cikinsu," in ji Hafsat.
KU KARANTA: Yadda za ka yi rajista ta yanar gizo domin zuwa yin allurar rigakafin korona cikin sauƙi
A cewar ta, ƴan bindigan sun saka kaya irin na sojoji, sun ce sun fi karfin jami'an tsaro tunda sun shiga makarantar sun sace mata.
Hafsat, wadda ta ce ta yi murna bisa sako su da aka yi ta ce zata cigaba da karatu a makarantar amma na jeka-ka-dawo.
NAN ta ruwaito cewa an sace ɗaliban ne misalin ƙarfe 2 daren Alhamis wadda hakan ya janyo hankalin jama'a inda da dama suka yi ta kira ga gwamnati ta ce to su
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng