Kungiyoyi 28 su na so sabon Shugaban EFCC ya fara da binciken ‘satar’ tsohon Gwamnan APC

Kungiyoyi 28 su na so sabon Shugaban EFCC ya fara da binciken ‘satar’ tsohon Gwamnan APC

- Wasu kungiyoyi su na so EFCC ta binciki tsohon Gwamnan Zamfara

- An bukaci Abdulrasheed Bawa ya yi karin-kumallo da Abdulaziz Yari

- Ana jifar Gwamnatin Yari da zargin sace N22.5bn tsakanin 2011-2019

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu, sun roki shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya fara bincike a kan zargin da ke kan wuyar Abdulaziz Yari.

Ana zargin tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, da wawurar Naira biliyan 22.5 da gwamnatinsa ta ware na ayyuka a lokacin da yake mulki.

Wani jami'in wannan kungiya, Kwamred Olufemi Lawson, ya fitar da jawabi ya na zargin gwamnatin Yari da karkatar da kudin da za ayi wa jama’a aiki.

Olufemi Lawson yake cewa kungiyarsu ba ta ji dadin yadda tsaro ya tabarbare musamman a Arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma jihar Zamfara.

KU KARANTA: Kungiya ta bankado badakaloli a cibiyar NARICT, ta sanar da hukuma

Lawanson a madadin kungiyoyin ya ce ba za su yi gum yayin da masu mulkin da aka zaba su ke watsi da al’ummarsu, su ka gaza sauke nauyin da ke kansu ba.

Wadannan kungiyoyi su ka ce ‘yan bindiga sun addabi Zamfara ne saboda gazawar gwamnonin jihar, su ka ce Abdulaziz Yari ya tare ne a Abuja da yake mulki.

A cewar gamayya kungiyoyin, badakaloli gwamnatin Yari da aka gano ya sa ake ta kokarin tunzara mutanen garin Gusau su rika sukar gwamnatin da ke ciki.

Wannan gamayya ta tara kungiyoyi 28 ta yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Fubrairu, 2021 a Legas, ta na tuhumar gwamnatin Abdulaziz Yari.

Kungiyoyi 28 su na so sabon Shugaban EFCC ya fara da binciken ‘satar’ tsohon Gwamnan APC
Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari Hoto: Naijanews
Source: UGC

KU KARANTA: Yahaya Bello ya yi zama da tsohon Shugaban kasa Obasanjo a Abuja

Abdulaziz Yari ya yi mulki ne tsakanin 2011 da 2019 a karkashin jam'iyyar APC mai mulki.

Kwanaki kun ji yadda Abdulaziz Yari ya bayyana a babban ofishin EFCC da ke Legas, ya sha dogayen tambayoyi a ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 2021.

Alhaji Abdulaziz Yari ya hallara ofishin EFCC ne domin amsa goron gayyatar da aka aika masa bayan ya yi yunkurin cire Naira biliyan 300 daga asusun banki.

Daga baya Abdulaziz Yari ya bar ofishin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, amma ba a wanke shi daga zargi ba tukuna.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel