Yadda Shugaban NARICT ya ke tafka barna iri-iri– Kungiya ta rubutawa Gwamnatin Buhari takarda

Yadda Shugaban NARICT ya ke tafka barna iri-iri– Kungiya ta rubutawa Gwamnatin Buhari takarda

Kungiyar Network for Justice ta rubuta takardar korafi zuwa ga CCB, ta na zargin darekta janar na ma’aikatar NARICT da saba doka da ka’idojin aiki a ofis.

Legit.ng Hausa ta samu dogon korafin da CCB ta rubuta a kan shugaban ma’aikatar bincike ta NARICT da ke Zaria, ta ce shugaban ya na son kai da kabilanci.

Daga zargin da kungiyar ta ke yi a kan Farfesa Jeffrey Tsware Barminas, akwai ikirarin ba ya bin doka da sanin aiki wajen tura ma’aikata zuwa sassan ma’aikatar.

Kungiyar N4J ta zargi shugaban na NARICT da rashin gaskiya, ta ce ana cire kudin hayar gidajen ma’aikata, ana karkata kudin zuwa wani asusu (a madadin TSA).

KU KARANTA: Watakila Abdulrasheed Bawa ya na da alaka da Ministan shari’a - Sagay

Network for Justice ta bada misali da wata ma’aikaciya da aka dauka aiki a asibitin NARICT a shekarar 2017, amma kafin a je ko ina aka sauya-mata wuri aiki.

Kungiyar ta ce an dauke wannan mata zuwa jihar Benuwai bayan ta yi aure, amma har yau ba ta sake dawowa wurin aikin na ta ba, wanda hakan ya saba wa doka.

Haka zalika a karkashin jagorancin Farfesa Jeffrey Tsware Barminas an yi wa babban jami’in tsaro karin matsayi duk da ana zargin ya na amfani ne da takardun ogi.

Bugu da kari, wannan kungiya ta ce kudin da ake ware wa cibiyar, ya fi karfin aikin da ake gani a kasa.

Yadda Shugaban NARICT ya ke tafka barna iri-iri a ofis – Kungiya ta fadawa Gwamnatin Buhari
Takardar korafi a kan shugaban NARICT
Asali: Original

KU KARANTA: Bai kamata sabanin Gwamnoni ya bayyana a waje ba – NEF

A korafin mai shafuka barkatai, Network for Justice ta hannun Auwalu Inusa, ta ce akwai ma’aikatan da aka samu da laifi wajen jarrabawa, amma har gobe su na ofis.

Akwai zargin ma’aikatan da ya kamata su yi ritaya bayan sun zarce shekarun aiki, amma su na ofis, daga ciki har da babban jami’in binciken kudi da ya haura shekara 60.

CCB ta samu takardar wannan korafi wanda aka ambaci Darektan gudanar wan a ma’aikatar Ocheme Ogabidu, da hannu a wannan barna duk da ya isa shekarun ritaya.

Sauran wadanda aka sanar sun hada da fadar shugaban kasa, AGF, DSS, SGF, gwamnatin Kaduna, Ministan kimiyya, kwamitocin majalisa da majalisar Kaduna da masarautar Zazzau.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel