Gwamnan Kogi da ake jita-jitar zai nemi kujerar Buhari a 2023 ya sa labule da Obasanjo

Gwamnan Kogi da ake jita-jitar zai nemi kujerar Buhari a 2023 ya sa labule da Obasanjo

- Gwamna Yahaya Bello ya zauna da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Gwamnan ya cigaba da tsare al’umma

- Alamu na nuna Yahaya Bello zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023

A ranar Lahadi, 28 ga watan Fubrairu, 2021, tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gana da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an yi wannan zama ne ta bayan labule a babban birnin tarayya Abuja.

Hadimin gwamnan jihar Kogi, Mohammed Onogwu, ya bayyana yadda wannan zama tsakanin Mai gidansa da tsohon shugaban Najeriyar ta kasance.

Mohammed Onogwu yake cewa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamna Yahaya Bello ya cigaba da kokarin da yake na samar da tsaro a jiharsa ta Kogi.

KU KARANTA: Fastocin neman shugaban kasar Bello sun bazu har Adamawa

“Tsohon shugaban kasa, Obasanjo, ya bayyana cewa a kokarin da ake yi na yaki da rashin tsaro, dole sai kowa ya tashi tsaye an yi da shi.” Inji Onogwu.

Obasanjo wanda ya mulki kasar nan na tsawon shekara takwas tsakanin 1999 da 2007 ya ce gwamnoni su yi amfani da kowa wajen yakar rashin tsaro.

Gwamna Bello da ake yi wa hangen takara a zaben 2023, ya gode wa Obasanjo na irin dattakun da ya nuna, ya ce ‘yan-baya za su iya koyi da dinbin hikimarsa.

Kafin nan, gwamnan ya hadu da tsofaffin taurarin Super Eagles ya yi kira a gare su da su yi watsi da kiran da ake yi na cewa shugaban kasa ya fito daga Kudu.

Gwamnan Kogi da ake jita-jitar zai nemi kujerar Buhari a 2023 ya sa labule da Obasanjo
Yahaya Bello da Obasanjo Hoto: Dele Momodu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kungiya ta jadadda goyon bayanta ga Yahaya Bello a 2023

Yahaya Bello ya bukaci ‘Yan Najeriya su zabi ‘dan takarar da ya cancanta a zaben 2023, a maimakon a rika kallon yankin da ya fito, kabilarsa da addininsa.

Kwanakin baya Gwamnan Kogin, kuma shugaban kwamitin jan hankalin matasa zuwa APC, Yahaya Bello, ya yi ikirarin cewa Femi Fani Kayode zai koma APC.

Yahaya Bello a wani taron jam'iyyar APC ya bayyana cewa su na jawo hankulan 'yan siyasa ba tare da la'akari da irin abubuwan da suka aikata a lokutan baya ba.

Daga baya tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya yi zamansa a PDP.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel