Satar 'yan makaranta: Hadimin Ganduje yace Buhari ya kawo karshen ta'addanci ko yayi murabus
- Hadimin Ganduje, Salihu Yakasai ya bukaci Buhari ya kawo karshen ta'addanci ko yayi murabus
- Yakasai ya ce wannan babban abun kunya ne da gwamnatin APC ta gaza baiwa rayuka da dukiyoyi kariya
- Dawisu ya wallafa hakan ne yayin yin martani ga satar 'yan matan makarantar Jangebe da aka yi
Hadimin Gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Yakasai, ya bukaci gwamnatin APC ta shawo kan ta'addanci ko kuma tayi murabus.
A wallafar da Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu yayi a shafinsa na Twitter bayan samun labarin satar 'yan matan daga makarantar Jangebe, ya bukaci gwamnatin APC da ta kawo karshen 'yan ta'adda ko tayi murabus.
A yau Juma'a, 26 ga watan Fabrairu ne arewacin Najeriya ta tashi da mugun labarin sake kwashe wasu 'yan mata a makarantar kwana da ke Jangebe ta jihar Zamfara.
KU KARANTA: Ba zan taba baiwa masu kiran Fulani da 'yan ta'adda hakuri ba, Gwamnan Bauchi
Mummunan lamarin ya faru wurin karfe 1 na dare yayin da 'yan bindiga suka tsinkayi makarantar.
"A bayyane yake a matsayinmu na gwamnatin APC mun gaza a kowanne mataki. Mun gaza ga 'yan Najeriya domin hakkinmu na farko bayan zabenmu shine baiwa rayuka da kadarori tsaro.
"Babu ranar da za ta fito ta fadi ba tare da an samu ire-iren haka ba a kasar nan. Wannan abun kunya ne. A yi maganin ta'addanci ko a yi murabus," ya wallafa.
KU KARANTA: Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu
A wani labari na daban, majalisar dattawa ta kare kanta a kan hukuncin da ta yanke na tabbatar da sabon shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.
Tabbatar da Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC ya faru ne a ranar Laraba jim kadan bayan ya bayyana gaban majalisar dattawan kuma sun tantancesa.
Tabbatar da Bawa tazo ne a lokacin da ake ta zargi tare da cece-kuce a kan rahoton cewa an taba kama sabon shugaban EFCC da laifin rashawa, Channels TV ta ruwaito.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng