Baicin shugabannin Najeriya gajiyayyu ne, da kurkuku ya kamata a jefa Sheik Gumi: Yan Jaridan Najeriya

Baicin shugabannin Najeriya gajiyayyu ne, da kurkuku ya kamata a jefa Sheik Gumi: Yan Jaridan Najeriya

Shugaban kungiyar yan jaridan Najeriya (NUJ), Chris Isiguzo, a ranar Juma'a ya mayar da martani ga Sheikh Ahmad Mahmud Gumi bisa kalaman da yayi na kwatanta yan jarida da yan bindiga.

Isiguzo wanda yake magana a madadin yan jaridan Najeriya ya ce baicin shugabannin Najeriya gajiyayyu ne, da tuni an jefa Sheikh Ahmad Gumi cikin Kurkuku.

Ya kara da cewa kalaman da Gumi ke yi na nuna goyon baya ga yan bindiga na nuni ga cewa yana da wata manufa ta musamman.

Zaku tuna cewa a ranar Laraba, Sheikh Gumi ya ce yan jarida su daina kiran yan bindiga da sunan masu laifi saboda su kansu masu laifi ne.

Amma, Isuguzo ya ce wannan maganar banza ce saboda babu wani abun kwatantawa tsakanin aikin jarida da ta'addanci.

"A kasashen da aka cigaba, cikin kurkuku za'a jefa Sheikh Gumi, saboda ba ma'aikacin gwamnati ba ne. Amma saboda gajiyawan shugabanninmu, yana cigaba da kalaman da ya ga dama kuma yana shiga cikin yan bindiga yadda yake so," Isiguzo yace.

"Kiran yan jarida da sunan masu laifi na nun acewa Sheikh Gumi ya tona asirin kansa a matsayin mutum mara hakuri wanda ba zai so a binciki abubuwan da yake yi ba."

DUBA NAN: Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga

Baicin shugabannin Najeriya gajiyayyu ne, da kurkuku ya kamata a jefa Sheik Gumi: Yan Jaridan Najeriya
Baicin shugabannin Najeriya gajiyayyu ne, da kurkuku ya kamata a jefa Sheik Gumi: Yan Jaridan Najeriya Hoto: Shafin Sheik Ahmad Gumi
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni

Sheikh Gumi ya shiga aikin da'awa ga yan bindiga don su daina aikata laifukan kashe-kashe da garkuwa da mutane.

A ziyarar karshe da yayi, Gumi ya shiga dajin Tegina inda ya gana da shugaban yan bindiga, Dogo Gide, kuma yace sun amince da wa'azinsa.

A jawabin hadimin Malamin, Salisu Hassan Webmaster, ya saki kuma Legit ta samu, ya yi nasiha ga yan bindigan kan muhimmancin sulhu.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel