Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni

Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni

- Buhari ya bayyana matsayarsa kan batun baiwa yan bindiga kudin fansa

- Wannan ya biyo bayan jawabin gwamnan Neja wanda yace Buhari yayi watsi da shi

- An sako daliban makarantar Kagara da aka sace mako guda da ya gabata

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce abinda wasu gwamnoni ke yi na baiwa yan bindiga kudi da motoci na da mumunan hadari.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin tsokaci kan sace dalibai mata a makarantar sakandaren GGSS Jangebe a jihar Zamfara.

Buhari ya ce sam ba zai taba amincewa da irin wannan garkuwa da dalibai da akeyi ba.

A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya saki, Buhari ya yi kira ga gwamnoni su daina baiwa yan bindiga kudade da motoci.

Buhari ya ce yana kira ga gwamnoni su canza abinda sukeyi na azurta yan bindiga da kudade da motoci, kuma ya gargadesu cewa hakan na da hadari.

Hakazalika ya ya baiwa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su inganta tsaro a makarantu.

KU KARANTA: Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga

Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni
Ku daina baiwa yan bindiga kudi ya na da hadari, Buhari ya gargadi gwamnoni Credit: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga

A bangare guda, cikin yunkurin ceto dalibai mata 317 da aka sace ranar Juma'a, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya nemi taimakon tubabbun dan bindiga Auwalu Daudawa da Zakoa Buhari, ThisDay ta ruwaito.

Auwalu Daudawa ne dan bindigan da ya jagoranci satan daliban makarantan sakandaren GCSS, Kankara, a jihar Katsina.

Zakoa Buhari kuma shine dan shahrarren kasurgumin dan bindiga, Buhari Daji.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel