Sheikh Gumi ya zauna da Dogo Gide, shugaban yan bindiga a dajin Tagina, jihar Neja

Sheikh Gumi ya zauna da Dogo Gide, shugaban yan bindiga a dajin Tagina, jihar Neja

- Sheikh Ahmad Gumi ya shiga dajin Tagina domin ganawa da yan bindiga

- Malamin ya shahara da shiga daji don tattaunawa da yan bindiga

- Gwamnan Neja ya karbi bakuncin Sheikh Gumi ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar

Dirarsa jihar Neja ke da wuya, babban Malamin addini, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya shiga daji domin ganawa da yan bindiga a dajin Tagina, dake iyakan jihar Neja da Birnin Gwari a Kaduna.

A jawabin hadimin Malamin, Salisu Hassan Webmaster, ya saki kuma Legit ta samu, ya yi nasiha ga yan bindigan kan muhimmancin sulhu.

Yace: "Alhamdullah! Yau Allah ya taimaki Dr. Ahmad Gumi da tawagarshi samun damar ziyartar garin Mina inda ya isa Kontagora daga nan ya karasa dajin Tagina inda suka yi mahada da Shugaban Daji (Dogo Gide). Wannan daji ne da ya hada garin Niger da Kaduna ta wurin Birnin Gwari."

"Nasihohi daga bakin Sheikh Dr. Ahmad Gumi game da muhimmancin yin Sulhu da kuma haramcin yaki a wannan wata da kuma rokonsu game da ajiye makamai da haramcin yin fasadi a bayan kasa."

DUBA NAN: Yan sanda sun fara sintiri da jiragen sama don gano daliban da aka sace a Kagara

Sheikh Gumi ya zauna da Dogo Gide, shugaban yan bindiga a dajin Tagina, jihar Neja
Sheikh Gumi ya zauna da Dogo Gide, shugaban yan bindiga a dajin Tagina, jihar Neja Credit: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

DUBA NAN: Rashin tsaro ya zama kasuwanci ga wasu 'yan Nigeria, in ji Solomon Dalung

Ya kara da cewa, shugaban yan bindigan ya bayyanawa Malamin da tawagarsa cewa ya amince da nasihar da akayi masa kuma zai yi amfani da shi.

Hakazalika ya gabatar da abubuwan da suke bukata domin ajiye makamansu.

Yace: "A nashi jawabin Dogo yace wannan shine zama na farko da aka yi da shi game da irin wannan sulhun kuma ya yarda ya dauka, kuma yana shaidawa malam zai fara aiwatar da wadansu."

"Dogo Gide ya shaidawa malam irin abubuwan da suke nema wanda idan aka yi musu shi zasu saki mutanen da suke hannunsu."

A bangare guda, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aikin ceto ta sama don ceto daliban da aka sace, malamai, da sauran ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.

Kakakin ‘yan sanda, Frank Mba, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa mai taken: Satar Kagara: Mun dukufa wajen ganin mun kubutar da duk wadanda aka sace, in ji IGP’, a ranar Alhamis.

Mba ya kuma ce tuni aka fara sa ido a iska don ganin an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel