Hotunan daliban Karaga bayan sun kwashe kwanaki 9 hannun yan bindiga
- Dalibai da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara sun gana da gwamnan Neja
- A safiyar yau ne aka tabbatar da sako daliban daga hannun 'yan bindigan da suka sace su
- Gwamnan ya basu shawara kada su fidda tsammanin samun ilimi
Daliban makarantar sakandaren kimiya da aka sace kwanaki tara da suka gabata a Kagarasun gana da gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, bayan kubutarsu daga hannun yan bindiga.
Mutum 38 wanda ya hada da dalibai, malamai da 'yan uwansu sun samu yanci ne bayan zaman fiye da mako guda hannun bindiga.
Sakatariyar yada labaran gwamnan jihar, Mary Noel Berje, ta bayyana cewa gwamnan ya karbi bakuncinsu a gidan gwamnatin jihar dake, Minna.
Ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Asabar a shafinta na Facebook.
A cewarta, gwamna Bello ya godewa Allah bisa nasarar cetosu daga hannun miyagun.
Ya shawarci daliban kada su gajiya wajen neman ilimi kuma su dauki wannan matsayin ibtila'i na rayuwa.
Ta kara da cewa cikin mutum 38 da aka saki, 24 dalibai ne, 6 malamai ne, kuma 8 yan uwan malaman ne. Amma daya daga cikinsu ya fadi rashin lafiya sakamakon gajiya.
Kalli hotunansu:
KU KARANTA: Bayan kulle makarantun sakandare, gwamnatin Kano ta kulle wasu makarantun kwaleji 4
DUBA NAN: Hukumar kare hakkin yara ta ƙasa ta ba wa gwamnan Zamfara shawara
Mun kawo muku cewa dalibai tare da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja sun isa babban birnin jihar, Minna.
Dalibai 27, malamai 3 tare da wasu mutum 12 ne aka sace yayin harin da aka kai makarantar. A wani bidiyo, an ga daliban suna fitowa daga dajin.
An gano cewa an nadi bidiyon a wurin makarantar sakandare na Attahiru da ke Madaka a jihar Neja.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng