Farfadowar tattalin arziki: Babu wani canjin da talaka zai gani, kawai rubutun takarda ne, Dakta Adamu

Farfadowar tattalin arziki: Babu wani canjin da talaka zai gani, kawai rubutun takarda ne, Dakta Adamu

- A watannin ukun karshe na shekarar 2020, alkaluma sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya farfado

- Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na cewa hakan ba ya nufin dan Najeriya zai ga wani sauyi

- A ranar Alhamis aka shirya zama da shugaban kasa kan shirin kara farashin litan man fetur

Masanin tattalin arziki, Dakta Ahmed Adamu, ya bayyanawa cewa talakan Najeriya ya cire tsamannin cewa labarin farfadowar tattalin arziki wani abin farin ciki ne.

A zantawar da wakilin Legit hausa tayi da shi, Dakta Adamu, wanda Malami ne a tsangayar tattalin arziki a jami'ar Nile dake birnin tarayya Abuja, yace babu wani canjin da talaka zai gani.

A cewarsa, kawai rubutun takarda ne da ya shafi yan Boko da yan jarida amma babu wani tasiri da hakan zai yi a kan talakan Najeriya.

Dakta Adamu ya kara da cewa yanzu haka farashin litan man fetur na gab da sake hauhawa saboda tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

"Shi dai talakan Najeriya sai da yaji a labarai cewa tattalin arziki ya durkushe ko ya tashi, amma shi talakan Najeriya dama tattalin arzikinshi a durkushe yake. Ko na Najeriya ya tashi ko bai tashi ba nashi a kwance yake," Dakta Adamu yace.

"Iyaka yan Boko ne da yan jarida da wadanda suka san alkaluman da ake amfani da shi wajen kayyade tattalin arziki ne suka san fadi ko tashinsa."

"Shi talaka idan ya tashi da safe, babu kudin abincin da zai ci, tattalin arzikinshi a durkushe yake. Ko da ko tattalin arzikin Najeriya na kan alkalami takwas ne ko shida, shi a wajenshi zero ne."

DUBA NAN: Zulum ya rabawa mutane 34,000 kayan abinci da kudi sama da milyan dari

Farfadowar tattalin arziki: Babu wani canjin da talaka zai gani, kawai rubutun takarda ne, Dakta Adamu
Farfadowar tattalin arziki: Babu wani canjin da talaka zai gani, kawai rubutun takarda ne, Dakta Adamu Credit: Channels TV/Presidency
Asali: UGC

KU KARANTA: Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu

Daka Adamu ya cigaba da cewa a kamata a daina duba wadannan alkaluman, a rika duba ainihin tattalin arzikin talakawa wanda ya hada ruwan sha, wutan lantarki da tsaro.

A cewarsa, yanzu tsaro ya zama abinda dole sai mutum ya samawa kansa.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kaso 0.11 a cikin zangon ƙarshe na shekarar 2020.

"Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 0.11 bisa dari a zango na hudu na shekarar 2020, wanda ke wakiltar ci gaban farko a cikin zango uku da suka gabata," cewar rahoton.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel