Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu

Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu

- Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa zai tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

- Masanin tattalin arziki kuma malami, Dr Ahmed Adamu ya ce sam ba a kamo hanyar hakan ba a kasar nan

- A cewarsa, abinda ba a fara ba a cikin shekaru shida, ai bai dace a sa ran cewa za a same shi ba cikin shekaru biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa babu gudu balle ja da baya, mulkinsa zai fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci.

Sai dai kuma, 'yan Najeriya suna ta guna-gunin cewa basu ko alamar hakan ba.

Jaridar Legit.ng ta samu nasarar zantawa da Dr. Ahmed Adamu, tsohon hadimi ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar. Malami ne a jami'ar Nile da ke babban birnin tarayya, Abuja.

A matsayinsa na masani a fannin tattalin arziki, Legit.ng ta bukaci jin ta bakinsa a kan wannan ikirarin ko mai yuwuwa ne ko kuwa akasin hakan.

KU KARANTA: Ka zo mu tattauna, baka son kawo zaman lafiya, 'Yan bindiga sun gayyaci Buhari

Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu
Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu
Source: Original

Dr Ahmed ya ce hakan fade-fade ne kuma jita-jita ne. Lokacin da ake yakin neman zabe an tabbatarwa da jama'a cewa za a tsamosu daga cikin talauci.

A cewar masanin, duk an saba jin irin wadannan zantukan daga bakin 'yan siyasa. Abinda ba a yi a cikin shekaru shida ba zai yuwu a yi shi cikin shekaru biyu ba.

"Duk fade-fade ne tare da jita-jita. Lokacin da ake yakin kamfen na wannan jam'iyyar an dinga cewa za a fitar da mutane cikin talauci.

"A maimakon fitar da mutane, sai kara dilmiyar da mutane ake yi cikin talauci. Magana ce shaci fadi, idan na ga dama zan iya cewa zan muku famfon fura, zan muku famfon abinci. Duk magana ce kawai. Mu gani a kasa.

"Shekara wurin shida kenan ana mulki. Toh har yanzu ana cewa za'a, za'a. Abinda ba a yi ba cikin shekara shida, kada a sa ran za a yi cikin shekaru biyu. Fadi ne na 'yan siyasa. Bana ganin an dauka hanyar tsamo mutane daga talauci," Cewar masanin.

KU KARANTA: Ba zan taba baiwa masu kiran Fulani da 'yan ta'adda hakuri ba, Gwamnan Bauchi

A wani labari na daban, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Dr. Fatima Atiku Abubakar ta karyata ikirarin cewa ta yi sabunta rijistar zama cikakkiyar 'yar APC.

A wata takarda da ta fitar da kanta kuma ta saka hannu sannan ta baiwa manema labarai a ranar Laraba, Dr.Fatima ta ce zamanta 'yar APC a baya saboda bukatar gwamnatin Bindo na jihar Adamawa ne, Vanguard ta wallafa.

"Akasin rahotanni da ke yawo, ban sabunta rijistar APC ba. A 2015 lokacin da aka nada ni kwamishinan lafiya ta jihar Adamawa yasa na koma jam'iyyar mai mulki. Hakan ya zama dole in zan yi aikin."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel