Da ɗuminsa: Tattalin arziƙin Nigeria ya farfaɗo, an samu ƙarin kaso 0.11

Da ɗuminsa: Tattalin arziƙin Nigeria ya farfaɗo, an samu ƙarin kaso 0.11

- Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki inda ta samu ƙarin kaso 0.11 cikin dari a zangon ƙarshe na 2020

- Hakan ya biyo bayan janye dokar takaita zirga-zirga da hada-hadar kasuwanci na gida da waje

- Duk da cewar yana da rauni, hakan ya nuna cewa tattalin arzikin kasar na farfadowa sannu a hankali

Tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kaso 0.11 a cikin zangon ƙarshe na shekarar 2020.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Gwamnan Arewa ya zargi takwarorinsa da yin sakaci da aikinsu

"Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 0.11 bisa dari a zango na hudu na shekarar 2020, wanda ke wakiltar ci gaban farko a cikin zango uku da suka gabata," cewar rahoton.

Da ɗuminsa: Tattalin arziƙin Nigeria ya farfaɗo, an samu ƙarin kaso 0.11
Da ɗuminsa: Tattalin arziƙin Nigeria ya farfaɗo, an samu ƙarin kaso 0.11 Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

"Koda yake yana da rauni, ci gaban da aka samu yana nuna yadda ayyukan tattalin arziki ke dawowa sannu a hankali biyo bayan cire dokar takaita zirga-zirga da kuma takaita ayyukan kasuwanci na cikin gida da waje a zangon da suka gabata.

“A sakamakon haka, yayin da bunkasar Q4 2020 ya yi kasa da na bunkasar da aka samu a shekarar da ta gabata da kashi –2.44, ya karu da kaso 3.74 idan aka kwatanta da Q3 2020.

“A abunda akan samu kwata bayan kwata, ainihin bunkasar GDP ya karu da kashi 9.68 cikin dari wanda ke nuna ci gaba a karo na biyu a jere na ainahin bunkasar da aka samu a cikin shekarar 2020 bayan akasin da aka samu a zango biyu.

"Gaba ɗaya, a cikin shekarar 2020, an kiyasta ci gaban da aka samu a GDP na shekara-shekara da -1.92 bisa ɗari, raguwar kashi -4.20 idan aka kwatanta da kashi 2.27 da aka samu a shekarar 2019."

An samu kimanin gangar mai miliyan 1.56 a kowace rana a cikin zango huɗu na 2020; 0.11 ƙasa da abunda aka samu a zango na uku, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan fashi za su dandana kudarsu yayin da IGP ya tura dakaru na musamman 302 zuwa jihar Kaduna

A kan shekara-shekara, bangaren mai ya bunkasa zuwa -19.76 bisa dari.

Bangaren mai ya ba da kashi 5.87 bisa ɗari na jimlar GDP a Q4 2020.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel