Zulum ya rabawa mutane 34,000 kayan abinci da kudi sama da milyan dari
- Kuma dai, gwamnan jihar Borno ya sake farantawa al'ummarsa rai
- Wannan karon, shugaban ya kai ziyara garin Dikwa, gari mai tarihi a kasar Borno
- A ziyarasa, mutane 34,000 sun samu kudi da kayan abinci
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis ya kai ziyara garin Dikwa inda ya rabawa al'ummar garin 34,000 kayan masarufi da kansa.
Mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis, 25 ga Febrairu, 2021.
A cewarsa, gwamnan ya raba kayan masarufi daban-daban ga iyalai 34,00.
Ya kara da cewa an rabawa mata 23,000 kudi N115m akan dubu biyar-biyar, yayinda aka rabawa mazajensu buhun shinkafa, buhun wake, buhun masara. da man gyada.
Ya ce hakan na cikin shirin da gwamnatin jihar taimakawa marasa galihu da rikicin Boko Haram ya hanasu harkokin kasuwancinsu.
Bayan raba kayan abincin, Zulum ya kai ziyara asibitoci biyu dake garin Dikwa don jajantawa marasa lafiya, Gusau ya kara.
KU KARANTA: Ba zan yi wa ƴan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari
DUBA NAN: Tsaro: Gwamnoni da Sarakunan Arewacin Najeriya gaba daya sun hadu a Kaduna
A bangare guda, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce Fulani ba ‘yan ta’adda ba ne.
Ya fadi haka ne a Abuja jiya yayin ziyarar girmamawa ga ma'aikatan gudanarwa da sauran ma'aikatan Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON).
“Na riga na tsaya a kan wannan; mu ba 'yan ta'adda bane ba kuma masu aikata laifi ba. Tabbas, akwai 'yan ta'adda a tsakaninmu kuma hakan bai sanya dangi ko dukkan musulmai a matsayin masu aikata laifi ko yan ta'adda ba.," yace.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng