NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol kimanin miliyan 2 cikin kwantena a Legas

NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol kimanin miliyan 2 cikin kwantena a Legas

- Jami'an hukumar NDLEA sun kama kwantena dauke da kwayar Tramadol a Apapa jihar Legas

- Har wa yau, jami'an na NDLEA sun kai sumame wurare daban-daban a Legas sun kama mutum 90 da ake zargi

- Shugaban NDLEA na kasa, Brig Janar Buba Marwa ya jinjinawa jami'an ya kuma bukaci su cigaba da jajircewa

Hukumar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wata kwantena cike da kwayar Tramadol a tashar Apapa da ke jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan jami'an na NDLEA sun kama mutane 90 ciki har da dan kasar Indiya yayin sumamen da suka kai wa wasu masu safarar miyagun kwayoyi a sassan Legas inda suka kama kwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 614.396.

NDLEA ta kama kwantena maƙare da Tramadol a tashar Apapa
NDLEA ta kama kwantena maƙare da Tramadol a tashar Apapa. Hoto: #daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC

Shugaban sashin watsa labarai na hedkwatar NDLEA a Abuja, Femi Babafemi, a ranar Laraba a Abuja ya ce an kwace kimanin kwayoyi miliyan 2 na Tramadol (kwayoyi 1,994,400) da aka shirya cikin kwantena da aka yi karyar cewa tile ne.

Babafemi ya ce Kwamadan hukumar NDLEA na Tashar Apapa, Mr Samuel Gadzama ya ce an kama wata kwantenar dauke da miyagun kwayoyin a Kenya.

Gadzama ya ce, "Duk da cewa kwantena ta biyun ta iso Nigeria jami'an mu masu saka ido sun gano kwayoyin yayin bincike da suke yi a jirgin ruwan. Muna cigaba da bincike."

KU KARANTA: Masu garkuwa sun bi babban manomi har gida sun sace shi a Abuja

Kazalika, Babafemi yace rundunar NDLEA ta Legas ta kai samame wasu wurare a Agege, Ikorodu, Lekki, Okokomaiko da wasu sassan jihar ta kama wasu da ake zargin manyan dilalan miyagun kwayoyi ne.

Ya ce yayin sumamen an kama mutum 90 cikinsu har da wani dan kasar India sannan an kwato miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 614.

A bangarensa, Shugaban NDLEA, Brig Janar Buba Marwa (Mai murabus) ya yabawa kokarin jami'an ya kuma bukaci su cigaba da jajircewa a aikinsu.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel