Masu garkuwa sun bi babban manomi har gida sun sace shi a Abuja

Masu garkuwa sun bi babban manomi har gida sun sace shi a Abuja

- Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace wani babban manomi a Abuja

- Yan bindigan sun kai hari ne a kauyen Gafare inda suka tafi gidan manomin suka yi awon gaba da shi

- `Wani mazaunin garin ya ce tsakar dare masu garkuwar suka afka garin da makamaki suna ta harbe-harbe

Masu garkuwa da mutane sun sace wani manomi, sannan sun sace kayan abinci a ƙauyen Gafere a karamar hukumar Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin mai suna Yakubu ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi a lokacin da masu garkuwar suka afka garin suna harbe-harbe don firgita jama'a.

Masu garkuwa sun sace manomi, sun sace kayan abinci a Abuja
Masu garkuwa sun sace manomi, sun sace kayan abinci a Abuja. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: WhatsApp ta sanar da hukuncin da za ta yi wa waɗanda ba su amince da sabbin tsarinta ba

Ya ce masu garkuwar da ke ɗauke da makamai sun girke kansu a wurare daban daban a garin yayin da wasu daga cikinsu suka tafi gidan wanda suka sace.

Ya ce kai tsaye suka tafi har ɗakinsa suka tafi da shi, ya ƙara da cewa masu garkuwar sun sace kayan abinci daga gidan mutumin.

"Wasu mambobin kungiyar sun fasa shagunan mutane a ƙauyen sun sace kayan abinci da masarufi kafin su tafi da wanda suka sace," in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace surukar Alhaji Ɗahiru Mangal a Katsina

Majiyar Legit.ng ya gano cewa wanda aka sace babban manomi wanda ya dawo daga kasuwa bayan sayar da kayan abinci.

Kakakin ƴan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, bata amsa waya da sakon tes da aka aike mata ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164