'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC

'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC

- Yar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Fatima, ta sabunta rajistar ta na jam'iyyar APC a Adamawa

- Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Mista Ibrahim Bilar, shima ya tabbatar da sabunta rajistar

- Fatima, mai shekaru 49, ta rike mukamin kwamishinan lafiya a Adamawa a zamanin Gwamna Jibrilla Bindow

Daya daga cikin 'ya'yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar mai suna Fatima, ta sabunta rajistarta na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Trust ta ruwaito.

Fatima, tsohuwar kwamishiniyar lafiya a jihar Adamawa, ta yi rajista da jam'iyyar mai mulki a gunduma ta daya, mazaba ta 08 a karamar hukumar Jada na jihar Adamawa.

'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC
'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace surukar Alhaji Ɗahiru Mangal a Katsina

Shugaban jam'iyyar APC a jihar, Mista Ibrahim Bilar, shima ya tabbatar da rajistar na 'yar Atiku, Daily Trust ta ruwaito.

A baya, ta ce ba ta bi tsohon mataimakin shugaban kasar ba zuwa jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP).

An nada Fatima mai shekaru 49 a matsayin kwamishina a Augustan shekarar 2015 a karkashin gwamnatin tsohon gwamna Jibrilla Bindow.

KU KARANTA: 'Yan bindigan sun roƙi mu yafe musu', in ji wadanda aka sace a Neja

Mahaifinta ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a 2019. ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel