Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna

- Yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyuka a kananan hukuomin Igabi da Chikun a jihar Kaduna

- Yan bindigan sun halaka mutane kimanin 18, sun jikkata wasu sannan sun sace shanu tare da kone rumbum abinci

- A bangarensu, jami'an tsaro a jihar Kaduna sun bi sahun wasu daga cikin yan bindigan inda suka hallaka su tare da kai sumame wasu mabuyar yan bindigan

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe a kalla mutane 19 da wasu yan bindigan da ba a san ko su wanene ba suka kai a karamar hukumar Igabi na jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwa, ne ya bada tabbacin a ranar Laraba cikin sanarwar da ya fitar.

A cewar kwamishinan, an kashe yan bindiga da dama a wurare daban-daban.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

Ya kara da cewa a kauyen Anaba da ke karamar hukumar Igabi da aka kai hari, mutum bakwai sun rasu, sun hada da Ali Musa, Isa Sharehu, Tijjani Isa, Auwalu Shehu, Hashim Abdullahi, Hassan Saidu da Umar Rilwanu.

An kone gidaje da dama a garin tare da rumbuna. A kalla shanu guda 20 aka sace sannan an yanka kaji da dama an yi awon gaba da su.

DUBA WANNAN: WhatsApp ta sanar da hukuncin da za ta yi wa waɗanda ba su amince da sabbin tsarinta ba

Kazalika, a kauyen Barinje na karamar hukumar Chikun da aka kai hari an kashe mutane takwas, su ne Sunday Gwamna, Lawal Jizo, Salha Barau, Sabo Barau, Umaru Barau, Muhammadu Dan Azumi, Zailani Dogara da Jikan Gambo.

An kone gidaje da dama a garin tare da rumbuna. A kalla shanu guda 20 aka sace sannan an yanka kaji da dama an yi awon gaba da su.

Kazalika, a kauyen Barinje na karamar hukumar Chikun da aka kai hari an kashe mutane takwas, su ne Sunday Gwamna, Lawal Jizo, Salha Barau, Sabo Barau, Umaru Barau, Muhammadu Dan Azumi, Zailani Dogara da Jikan Gambo.

An sace wasu mutanen garin sannan an yi awon gaba da shanu yayin harin. Mutane da dama da suka jikkata suna asibiti ana musu magani.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun bi babban manomi har gida sun sace shi a Abuja

An hangi yan bindiga da dama a hanyar Kankomi, an bi sahunsu an kashe da dama cikinsu.

Kazalika, sakamakon bayannan sirri da aka samu, sojojin sama da na kasa sun kai sumame a dazuwan da ke tsakanin Maidaro da Damari.

An kuma kai wani sumamen a Goron Dutse bayan tabbatar da yan bindigan suna boe a dajin inda aka kashe da dama. Kazalika, an datse wasu yan bindigan a kan babura za su shiga daji a Kuyambana an halaka su.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasu kuma ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel