WhatsApp ta sanar da hukuncin da za ta yi wa waɗanda ba su amince da sabbin tsarinta ba

WhatsApp ta sanar da hukuncin da za ta yi wa waɗanda ba su amince da sabbin tsarinta ba

- Kamfanin WhatsApp ta ce masu amfani da manhajar da ba su amince da sabbin tsare-tsaren ta za su rasa damar amfani da manhajar

- Kamfanin ta ce za ta bawa masu amfani da manhajar dama har zuwa ranar 15 ga watan Mayun 2021 kafin dokar ta fara aiki

- WhatsApp ta ce sabbin tsare-tsaren da ta gabatar za su bawa masu kasuwanci damar biyan kudinsu ne amma kamfanin ba zai rika karanta sakonnin jama'a ba

Kamfanin manhajar sadarwa na WhatsApp mallakar Facebook ta sanar da hukuncin da za ta yi wa masu amfani da manhajar da suka ƙi amincewa da sabbin tsare-tsaren da ta ɓullo da su.

Kamar yadda ya ke a bayanin da ke shafin intanet na kamfanin, an bawa masu amfani da manhajar da ba su amince da sabbin tsarin ba zuwa ranar 15 ga watan Mayu su yi hakan ko kuma nasu ya dena aiki, rahoton The Nation.

WhatsApp ta sanar da hukuncin da za ta yi wa waɗanda ba su amince da sabuwar tsarinta ba
WhatsApp ta sanar da hukuncin da za ta yi wa waɗanda ba su amince da sabuwar tsarinta ba. Hoto: The Nation News
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace surukar Alhaji Ɗahiru Mangal a Katsina

Waɗanda hakan ta faru da su ba za su iya karanta saƙo ba a manhajar, a cewar kamfanin amma za su iya amsa kira kuma za su iya ganin alamar shigowar sabbin saƙonni amma hakan ma 'na gajeren lokaci'.

A hirar da aka yi da TechCrunch, kamfanin ya ce 'gajeren lokacin' zai kasance na makonni kafin a rufe shafinsu a ranar 15 a ga watan Mayu.

Masu amfani da manhajar na iya rasa saƙonnin su duba da cewa dokokin WhatsApp na wadanda suka dena amfani da manhajar ya ce "a kan goge saƙonni bayan kwana 120 sun shuɗe ba a yi amfani da manhajar ba".

Idan za a iya tunawa, a watan Janairu kamfanin ta fasaha ta sanar da cewa za ta aiwatar da canjin daga ranar 8 ga watan Fabrairun 2021.

KU KARANTA: Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA

Kamfanin ta jinkirta zartar da sabbin tsare-tsaren da watanni uku sakamakon damuwa da wasu masu amfani suka nuna kan yiwuwar bayanansu za su iya komawa shafin Facebook, wacce ita ke da WhatsApp.

Duk da cewa WhatsApp na iya ganin bayanai kamar lambobin wayar masu amfani da WhatsApp tun 2016, kamfanin ya tabbatar cewa "WhatsApp baya iya karanta saƙonnin ku domin akwai fasahar da ke kare hakan ta yadda masu saƙon kawai za su iya karanta abinsu."

WhatsApp ta ce wannan sabon tsarin zai bawa masu kasuwanci damar iya biyan kuɗi cikin sauƙi ne, a cewar TechCrunch.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164