Rashin tsaro: Sulhu da ƴan bindiga ba shine abinda ya fi dacewa ba, Abdulsalami Abubakar

Rashin tsaro: Sulhu da ƴan bindiga ba shine abinda ya fi dacewa ba, Abdulsalami Abubakar

- Tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) ya ce sulhu da yan bindiga ba shine abinda ya fi dacewa ba

- Abdulsalami Abubakar ya ce ya zama dole a inganta tsaro a dukkan sassan kasar ta yadda ɓata-gari ba za su samu daman aikata laifi ba

- Janar Abubakar ya kuma ce akwai bukatar al'ummar kasar su koma su so juna kamar yadda ake a baya ba tsangwama da ƙyama

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus) ya ce yin sulhu da ƴan bindiga ba shine hanyar da ya fi dacewa ba wurin kawo karshen fitinar, rahoton Channels Television.

Da ya ke magana ranar Talata bayan ganawa da kungiyar gwamnonin Nigeria a Minna, tsohon shugaba ya ce hanyar da ta fi dacewa don magance matsalar garkuwa da yan bindiga shine tun farko a hana aikata laifukan.

DUBA WANNAN: 'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC

Rashin tsaro: Sulhu da ƴan bindiga ba shine abinda ya fi dacewa ba, Abdulsalami Abubakar
Rashin tsaro: Sulhu da ƴan bindiga ba shine abinda ya fi dacewa ba, Abdulsalami Abubakar. Hoto: @thecableng
Source: UGC

Duk da ya amince wasu lokutan sulhu na da amfani don ceto wadanda aka yi garkuwa da su, Abdulsalami ya ce kasar na buƙatar tsaro mai inganci don dakile ayyukan ɓatagarin tun kafin su kai hari.

Da ya ke misali da sace yaran Kagara, Abdulsalami ya ce, "ko da wani ya san inda ɗaliban suke, rashin hikima ne a afka da yaƙi don ceto su," domin za a iya rasa rayukan wadanda ake son ceto.

Ya jadadda bukatar da ke da akwai na inganta tsaro a kasar don kare afkuwar hakan a gaba.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun bi babban manomi har gida sun sace shi a Abuja

A cewarsa, jami'an tsaro sun yi kaɗan a kasar don haka akwai bukatar goyon baya daga jama'a kuma da ɗaukan sabbin jami'an tsaro.

Janar Abdulsalami kuma ya koka kan yadda rashin yarda da juna ya wanzu a kasar inda yace dole mu koma yadda muke son juna a baya.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel