Ko a Amurka ana satar ƴan makaranta, in ji Lai Mohammed

Ko a Amurka ana satar ƴan makaranta, in ji Lai Mohammed

- Alhaji Lai Mohammed, Ministan sadarwa da al'adu na Nigeria ya ce ba a Nigeria ne kadai ake satar dalibai ba

- Lai Mohammed ya ce ko a kasashen da suka cigaba a duniya irinsu Amurka a kan samu irin wannan matsalar da satar yan makaranta

- Ministan ya jadada cewa gwamnati ba za ta biya fansa don karbo dalibai da malaman GSS Kagara ba amma tana amfani da wasu hanyoyin don ceto su

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ya ce ba a Nigeria kadai ake sace yan makaranta ba, ya kara da cewa a kan sace yan makaranta a mafi yawancin kasashen da suka cigaba har da Amurka.

Mohammed ya bayyana hakan ne yayin da aka gayyace shi a shirin 'News Watch' a Channels Television a ranar Litinin da The Punch ta bibiya.

KU KARANTA: Nan ba da daɗewa ba Boko Haram za su iya haɗewa da ƴan bindiga, Sheikh Gumi

Ana satar yan makaranta har a Amurka da sauran kasashen da suka cigaba, Lai Mohammed
Ana satar yan makaranta har a Amurka da sauran kasashen da suka cigaba, Lai Mohammed. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ba a yi wa Fulani adalci a Nigeria, in ji Mallam Isa Yuguda

Ministan ya kuma sake jaddada cewa gwamnati ba za ta biya kudin fansa ba domin sako dalibai da malaman kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara a jihar Neja. Ya kara da cewa gwamnati na amfani da hanyar tattaunawa da karfin bindiga don ganin an ceto wadanda aka sace.

Mohammed ya ce, "Ko a kasashen da suka cigaba a duniya, a kan sace yan makaranta. A bara, a Amurka, an sace yan makaranta har sau hudu, kuma wannan kasa ce da ke cikin wadanda suka fi cigaba a duniya."

Ministan ya ce su yan ta'adda dama sun fi kai hari ga wadanda ba za su iya kare kansu ba kuma sun san cewa satar yan makaranta zai janyo hankalin duniya.

"Sai mun yi takatsan-tsan, ba zai dace mu mayar da dukkan makarantun mu bariki ba. Abinda ke da muhimmanci shine tattara bayanan sirri a maimakon girke yan sanda da sojoji."

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel