Ba a yi wa Fulani adalci a Nigeria, in ji Mallam Isa Yuguda

Ba a yi wa Fulani adalci a Nigeria, in ji Mallam Isa Yuguda

- Tsohon gwamnan Bauchi, Mallam Isah Yuguda ya ce mutanen Nigeria ba su yi wa makiyaya fulani adalci

- Mallam Isah Yuguda ya yi wannan furucin ne a jihar Bauchi a ranar Lahadi bayan ya sabunta rajistarsa na jam'iyar APC

- A cewarsa, ba laifi bane idan gwamnati ta tallafawa makiyaya domin ta kan tallafawa manoma amma su makiyaya fulani an yi watsi da su

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda ya soki yadda ake ware makiyaya fulani ana danganta su da laifuka a Nigeria, Daily Trust ta ruwaito.

A hirar da ya yi da manema labarai bayan sabunta rajistarsa na jam'iyyar All Progressives Congress, a ranar Litinin a Bauchi, tsohon gwamnan ya ce ba a yi wa makiyaya fulani adalci a Nigeria.

Ba a yi wa Fulani adalci a Nigeria, in ji Mallam Isa Yuguda
Ba a yi wa Fulani adalci a Nigeria, in ji Mallam Isa Yuguda. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Har yanzu ba’a sako ɗalibai da malaman makarantar GSS Kagara ba

Ya ce, gwamnatin tarayyar ta yi watsi da makiyayan da ke samar wa kasar a kalla shanu miliyan daya a kowanne rana na tsawon shekaru.

A cewarsa, idan har gwamnati na ware makuden kudade a matsayin tallafi ga manoma, mai zai hana ta bawa makiyaya tallafin?

"Watsi da aka yi da Fulani musamman makiyaya wadda a yanzu suke bawa Nigeria a kalla shanu miliyan daya a kullum su yanke domin samun nama da irin rashin kyatatawa da jama'an Nigeria ke musu rashin adalci ne," in ji shi.

Tsohon gwamnan ya ce a lokacin da Lord Luggard ya gama cin Nigeria da yaki, makiyaya ne babban hanyar samun kudin shiga a kasar, "su suka samar da kudin da aka fara gina arewa har da jihar Benue da aka kore su yanzu."

KU KARANTA: Matar aure na neman saki saboda mijinta ya 'kasa yi mata ciki'

"Makiyaya ne su, su ke samar wa kasar nama kuma manoma suke. An saka jarin biliyoyin naira a noma, gwamnati na biyan tallafi kan takin zamani da sauransu, ka taba jin gwamnatin tarayya ta bawa manoma tallafi?

"Abinda na ke cewa shine Nigeria ba ta wa mutanen nan adalci. Lokacin da bature ya zo, ya girmama su domin sune hanyar samun kudin shigarsa, bayan haka ya samar musu hanyar shanu daga Maiduguri zuwa Otukpo, daga Sokoto zuwa Lokoja da Ilorin."

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel