Nan ba da daɗewa ba Boko Haram za su iya haɗewa da ƴan bindiga, Sheikh Gumi
- Sheikh Ahmad Mahmood Gumi ya ce akwai yiwuwar yan Boko Haram za s iya hadewa da yan bindiga
- Babban malamin ya ce akwai alamun cewa idan matsin lamba ya yi yawa kungiyoyin biyu za su iya yin hadin gwiwa
- Gumi ya ce akwai bukatar malaman addini su bada gudunmawa don ganin hakan bai faru ba a kasar
Malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya ce nan bada dadewa ba yan Boko Haram za su hade da yan bindiga da suka dade suna rikici da manoma a sassan kasar da ma fashi.
Gumi ya kuma ce makiyaya Fulani na ganin ana neman ganin bayansu don haka suke ketare kasashe domin su kare yan uwansu duk lokacin da aka kai musu hari, Vanguard ta ruwaito.
Babban malamin ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' da aka nuna a Channels Televsion a ranar Litinin.
Sheikh Gumi ya ce akwai bukatar malamai su shiga tsakani domin Fulani da wadanda ke yakarsu duk suna ganin kansu a matsayin makiya amma gaskiya shine dukkansu matsala guda ke damunsu.
A kan yiwuwar Boko Haram na amfani da Fulani, Gumi ya ce yan bindiga ba yan Boko Haram bane amma "Ya kamata muyi taka tsan-tsan.
"Idan matsin lambar ya yi yawa, ina ganin Boko Haram suna iya hadewa da Boko Haram. Mun ga alamun cewa Boko Haram za ta shige su."
Asali: Legit.ng