Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa

Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa

- Rikici ya barke tsakanin mayakan Boko Haram da na ISWAP a garin Sunawa

- An gano cewa ISWAP sun sace wasu mata ne masu alaka da Boko Haram

- Wurin kwato matan ne mayakan Boko Haram suka halaka na ISWAP masu yawa

Gagarumar arangama tsakanin Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da mayakan ISWAP ya kawo ajalin mayakan ISWAP masu tarin yawa, HumAngle ta ruwaito.

Gagarumin fadan ya faru ne a yankinsa tsakanin iyakar Nijar da Najeriya. Al-Thabat, wata kafar yada labarai mai alaka da al-Qaida ta bayyana.

A wata takarda da Al-Thabat ta fitar, ta ce Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram ta halaka mayakan ISWAP a wani kauye da ake kira da Sunawa tsakanin iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.

KU KARANTA: Shirye-shirye tare da al'adun da ke kunshe a bikin auren kasar Sudan

Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa
Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

BBC ta ruwaito cewa an fara rikicin ne bayan ISWAP ta yi garkuwa da mata masu tarin yawa wadanda ke da alaka da Boko Haram.

Babu bata lokaci kuwa Boko haram ta kai hari sansanin ISWAP din kuma ta ceto matan.

A shekarar 2016 ne bangaren Boko Haram na Shekau ya rabe daga ISWAP kuma tun daga nan suke ta samun hargitsi tare da hayaniya.

KU KARANTA: Gagarumar gobara ta lashe shaguna a kasuwar kayan gyaran motoci ta Kaduna

A wani labari na daban, mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da 'yan bindiga suka kai wasu anguwanni dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

A cewar Aruwan, 'yan sanda suna nan suna bincike akan yadda wasu matasa suka yi arangama da 'yan bindigan a anguwar. Fusatattun matasa sun kashe wane matashi da ake zargin ya hada kai da 'yan bindiga, The Cable ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel