Shirye-shirye tare da al'adun da ke kunshe a bikin auren kasar Sudan

Shirye-shirye tare da al'adun da ke kunshe a bikin auren kasar Sudan

- Sudan kasa ce wacce musulmai suka fi yawa, kuma al'adunsu da dokoki sun cigaba da wanzuwa tsawon zamani

- Bikin aure a Sudan yana daukar tsawon kwanaki kuma daga ango har amarya kowanne yana da rawar da ya kamata ya taka

- Aure a Sudan yana da bangarori muhimmai wadanda suka kasu kashi 3; sa rana, shirye-shirye da kuma shagalin bikin

Shagalin aure a kasar Sudan yana kwashe kwanaki da dama, inda ango da amarya suke taka rawa mabambanta.

Aure a Sudan yana da bangarori 3, sa ranar aure, shirye-shirye da kuma asalin shagalin bikin.

Sudan kasa ce wacce musulmai suka fi yawa, al'adu da shagulgulansu basu canza ba tsawon shekaru duk da dai akwai cigaba da aka samu na zamani.

Duk wasu shagulgula a bikin Sudan ana yin su ne kamar yadda musulunci ya tanada.

KU KARANTA: Da duminsa: Saraki da jiga-jigan PDP sun yi ganawar sirri da IBB, Abdulsalami

Shirye-shirye tare da al'adun da ke kunshe a bikin auren kasar Sudan
Shirye-shirye tare da al'adun da ke kunshe a bikin auren kasar Sudan. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

Sa ranar aure:

Ana sa ranar aure ne a Sudan bisa yadda dangin ango da amarya suka amince kuma hakan bai saba wa dokokin musulunci ba.

Ko dai ganin juna suka yi suka fara soyayya ko kuma hada su aka yi, iyayene suke zama don su tattauna lokacin da bikin zai kasance.

Angon yana gabatar da wani abu ne don kowa yasan yana neman aure zuwa ga dangin amaryar. A al'adance shanu ake kaiwa, amma yanzu kudi ake bayarwa.

Kai shanu dangin amarya yana nuna kulla ranar aure, lokacin bikin auren kuma sai angon ya karasa cikasa shanu don shagalin auren.

Shirye-shiryen aure:

Shirye-shiryen auren yana komawa kacokan gidan iyayen amaryar ne.

Gaba daya hankula suna karkata akan amaryar ne, kuma kawayenta da 'yan uwanta suna taruwa don shirin gyara fatar amaryar da inganta kyawunta kafin ranar auren.

Za a fara ne da gyaran gashin kanta da kuma kamsasa fatarta. Ana shagali ranar lalle don har minti ake rabawa kuma ana wake-wake yayin da ake zana fulawowi masu kyau a hannayen amarya da kafafunta.

A Sudan, sun yarda da cewa hakan yana korar shaidanun aljanu.

Shagalin daurin aure:

Ranar daurin auren, ango yana bayyana a gidan iyayen amarya, mahaifiyarta za ta gaishe shi kuma kamar yadda al'ada ta tanadar zai nemi izinin shiga gidan daga wurinta.

Bayan ta amince sai a yi masa iso zuwa ga amaryarsa da bakin da suka halarci bikin.

Daurin auren yana faruwa ne bayan ma'auratan sun sumbaci kafafun iyayensu don bukatar albarkarsu. Ana yi ana wakokin yabo da yi musu fatan alheri.

Daga nan za a tafi da ango da amarya zuwa gidan da za su zauna inda za a yi shagulgula kafin kowa ya watse.

KU KARANTA: Gaskiyar abinda ya faru tsakaninmu da Arewa24 a kan shirin Labarina, Malam Aminu Saira

A wani labari na daban, Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban PRTT yace zai iya rasa kafarsa indai ba a bashi damar zuwa asibiti neman magani ba, The Cable ta wallafa.

Dama Maina yana hannun hukuma akan zargin wawurar naira biliyan biyu na kudin fansho kuma ya tsere ya bar sanata mai wakiiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, a hannun hukuma bayan ya tsaya masa a matsayin tsayayye.

An samu nasarar damkarsa a jamhuriyar Nijar inda ya lallaba ya shige, a ranar 3 ga watan Disamban 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel