Arangama tsakanin 'yan bindiga da jama'a: Rayuka 3 sun salwanta a Kaduna

Arangama tsakanin 'yan bindiga da jama'a: Rayuka 3 sun salwanta a Kaduna

- Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Kajuru dake Kaduna

- Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Asabar

- A cewarsa, binciken 'yan sanda ya tabbatar da yadda wasu matasa suka yi arangama da 'yan bindiga a garin

Mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da 'yan bindiga suka kai wasu anguwanni dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

A cewar Aruwan, 'yan sanda suna nan suna bincike akan yadda wasu matasa suka yi arangama da 'yan bindigan a anguwar.

Fusatattun matasa sun kashe wane matashi da ake zargin ya hada kai da 'yan bindiga, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: A bar 'yan Najeriya su dinga yawo da makamai idan makiyaya suna yi, Fani-Kayode

Arangama tsakanin 'yan bindiga da jama'a: Rayuka 3 sun salwanta a Kaduna
Arangama tsakanin 'yan bindiga da jama'a: Rayuka 3 sun salwanta a Kaduna. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

Aruwan ya ce 'yan bindigan sun fara kai harn Unguwan Sha'awa, inda suka kashe wani Ubangida Dogo har cikin gidansa.

A cewarsa 'yan bindigan sun kai wani harin Ungwan Galadima har suka kashe wani Bulus Gwamna. Sannan sun kai hari Unguwan Gamu suka kashe wani Daniel Danlami.

"Har yanzu jami'an tsaro suna cigaba da bincike akan wani wanda ake zargin ya hada kai da 'yan bindiga yayin kai harin karamar hukumar Kajuru. Alamu sun nuna cewa sai da 'yan bindigan suka hada kai da wasu matasan garin kafin su kai harin," a cewarsa.

"Jami'an tsaro sun kara gano yadda suka kai wa wani da ake kira 'Doctor', dan kauyen Kujeni, wanda matasan Maro suka dauki fansa a kansa, ya bayyana hakan kafin mutuwarsa, inda yace akwai sa hannunsa a harin.

"Ya ambaci wani Fidelis Ali, dan Maro, a matsayin daya daga cikin wadanda suke hada kai da 'yan ta'addan. Tuni 'yan sanda suka kama Ali kuma yanzu haka yana hannunsu, " yace.

KU KARANTA: Gaskiyar abinda ya faru tsakaninmu da Arewa24 a kan shirin Labarina, Malam Aminu Saira

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai ya baiwa matasa shawarwari da dabarun da za su fatattaki tsofaffi irinsa daga siyasa.

A wata tattaunawa da 'Radio Now's Urgent Conversation' dake jihar Legas suka yi dashi a ranar Juma'a, ya yi kira ga matasa, kwararru a fannoni daban-daban da kuma shugabannin addini da su hada kawunansu wurin ciyar da siyasa da kasar nan gaba.

El-Rufai ya ce zanga-zanga da tayar da hankula ba za su kai kowa ko ina ba har sai mutanen kirki sun taru sun mika kawunansu ga taimakon kasarsu ta gado, Daily Trust ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: